KIRA GA MAGABATANMU: Sabbin Bidi’o’i Na Neman Hana Mu Yin Aure

Maganar gaskiya ya kamata Malaman mu da Sarakunan mu ku tashi tsaye don ganin an yaki wannan sabuwar bidi’a mai kokarin hanawa matasan mu yin aure da wuri. Domin Wannan abu ba addini ne ba, sannan kuma ba al’ada ba ce mai tushe ba. Amma kuma tana neman ta zama babbar barazana ga rayuwar matasan mu masu son yin aure da wuri.

Don haka mu ke kira ga shugabannin mu da su gaggauta shigowa a cikin wannan lamarin don ganin an dauki kwakwkwaran matakin hana yaduwar wannan mummunar Bidi’a a cikin al’umma. Wadda take neman zama babbar barazana ga matasan mu masu son yin aure da wuri don gudun fadawa ga aikata zinace-zinace.

Akwai ban haushi ace sai matashi ya yi wadannan bidi’o’i sannan matarsa zata shigo gidan sa;

1 Kayan mun gani muna So (See I Love) Kwali 30 zuwa 40 ko 50, da kuma kayan Sanyi kowace kala.

2 Kayan Lahe ( Akwati 13 zuwa 15)

3 Ranar Kauyawa (Kauyawa’s day)

4 Ranar Larabawa (Arab’s day)

5 Ranar Turawa (Europ’s day)

Da sauran bidi’o’i wadanda babu su a hadisi ko Qur’ani. Amman kuma suna neman su zamewa matasan mu wani babban kalubale dake kokarin hana su yin aure da wuri, har sai sun tara kudade masu yawa sannan zasu samu damar yin wadannan abubuwa.

To ina so in sanarda iyayen ya’ya mata cewa; Matukar ku ka kyale wannan mummunar dabi’a ta ci gaba, to wallahi ku kuma lalata ya’yanku da samari ke yi yanzu aka fara. Don haka ku saukakawa samari su auri ya’yanku tun kafin ya’yanku mata su kai wani matsayi na lalacewa.

Domin ko shakka babu, namiji ko macce matukar suka balaga to abu mafi kyau a gare su shine aure, domin duk macce mai lafiya ko namiji mai lafiya doli ne ya kasance kowa yana bukatar wani. Ta hanyar halal ko haram, sai dai wadanda Allah ya tsare kadai.

Ubangiji Allah ya bada ikon rushe wannan kazamar Bidi’a a cikin al’ummar musulmi.

Daga S-bin Abdallah Sokoto

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *