Abubuwan Da Suka Wajaba Namiji Ya Kula Da Su Lokacin Da Matarsa Ta Dauki Ciki

Jama’a Assalamu alaikum, dafatan kuna lafiya tare da iyalinku, kuma kuna biye da mu cikin filinmu mai albarka.

A wannan makon za mu tabo batun abubuwan da suka wajaba namiji ya kula da su daga lokacin da matarsa ta dauki ciki har zuwa bayan haihuwa.
Idan namiji zai jure kyautata wa iyalinsa lokacin ciki da haihuwa, haka nan ya zama wajibi ya bada gudunmowa a lokacin rainon abin da aka haifa, domin shi raino ba ya karewa har zuwa auran yaranmu duk alhakin na kanmu. Da zararar mace ta shiga kangin laulayi da renon ciki da kuma haihuwa wadda itama aba ce mai zaman da kanta, za a yi ta tanadin kudi a yi ta hakuri da tsarabe-tsarabenta, duk sanda akace ana da cikin nan a cikin kashe kudi ake da kawo kawo har Allah ya raba lafiya, idan an samu an haihu lafiya to an tsallake, idan ta zo da tangarda to sai an ji jiki da kashe kudi kuma a zo a yi hidimar suna shi ma idan ma’aurata basu kai zuciya nesa ba a kan samu rashin jituwa na kawo kawo, amma in an daure an yi daidai bukata to kowa cikin farin ciki zai kasance

Yana da kyau namiji ya san hakkinsa ne sayan kayan jariri daga kan sabulu har kayan tafiya asibitin amma wasu mazan basu damu da wannan ba sai abar mace na fafutakar yadda za ta yi, wannan yana jawowa mace rashin sukuni da rashin kwanciyar hankali har ta shiga hakkin abun da ke cikinta saboda tunaninta yaya za a yi ta samu wadannan kayan.

Amma idan namiji zai tallafa a bi abun cikin nutsuwa, to sha Allahu za a samar wa mace sauki, tunda sun wajabta a yi su din ko yayane dai a kamanta, ba sai mace ta je asibiti ba ana tambayarta ina kaza ina kaza abun kunya ne mai haihuwa ta je haihuwa babu abubuwan bukata. Wannan yana sa mace jin kunya cikin mutane ga surutu bayan tana neman samun lafiya sai kaga jini ya yi sama, yana da kyau maza su san wadannan abubuwan da ake bukata ga Asibiti.

Wasu zuwa asibitin ma bai dame su ba kawai don kar a ce su kawo sai su ce ai suma a gida aka haife su, da zamanin da da na yanzu ba ma daya ba ne, na da akwai kula daga iyaye maza, akwai cima mai kyau, akwai sa ido na miji ko iyayensa, sabanin na yanzu da son zuciya ya yi yawa wata ma uwar mijince za ta hana a kaita asibitin ko ta ce raki ne amma ba a tunanin sumatsin da ke cikin haihuwar da da ta yanzu.

Saka ido a kai mace asibiti shi ne domin kula da yanayin nakudar da lafiyarta gudun matsala, amma wasu mazan don rashin tausayi suna kai matan asibiti ake nemansu a rasa, idan iyayenki na da shi su yi in babu sai ka ga an rasa rai ko kuma an hadu da lalura wanda hakan bai dace ba.

Bayan haihuwa ana son a ci gaba da bawa mai jego kulawa ta cin abinci mai kyau, ba ta nama gashasshe mai yaji da dan ruwa-ruwa ko farfesu, ya kasance akalla ta yi sati tana cin abinci lafiyayye saboda wannan ma zama ne na jinya da shayarwa in ba ta ci ta ko shi ba, babu ta yadda za a yi yaronka (mijinta) ya samu ruwan nono mai kyau, ba fa ita kakewa ba danka kake wa saboda sai ta samu ta ci shi ma zai samu. Yanayin shayarwar mace yanayin abun da ta samu daga gidanka.

Saboda haka yana da kyau maza su dage da sanin mataki mataki na raino da tarbiyya.

Ita kuma mace ta kyautatawa kanta da gyara jikinta saboda ita haihuwa ba wasa bace dole sai an yi bikinta (jego) sannan za a samu lafiya

Wanka, shiga ruwan zafi, cin abinci mai kyau, samun bacci, shayar da jariri a kan kaida da bashi lokaci na sa jariri ya tashi cikin kumari da lafiya.

Zama cikin farinciki da annushuwa yana bawa maijego da yaronta lafiya, idan har za a kula da wadannan abubuwa to babu maganar rashin jin dadi kuma za ka samu farin cikin iyalinka, don haka a zurfafa tunani a kan meye ‘Reno’ .

  • Muhammad Baqeer Muhammad Baqeer

Daga Alkalamin Sadiya Garba Yakasai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *