Amaren Gulmawuya Na Watan Satumba Nura Da Hauwa (Ku Kalli Hotunan Gabanin Aurensu)


Labarin soyayyar Mohammad Nura Isah da masoyiyarsa Hauwa Suleiman kamar kowane irin labarin soyayya ne da kowa ya sani. Shi dai Ango Mohammad Nura Isah ya kasance dan asalin karamar hukumar Kontagora dake jahar Neja. Ya kammala digirinsa na farko a bangaren laburare da fasahar sadarwa daga jami’ar kimiyya da fasahar ta tarayya dake garin Minna a jahar Neja (FUTMIN). Ya yanzu haka shi malamin laburare a jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida dake Lapai (IBBU Lapai) a jahar Neja

Ita kuma amaryar Hauwa Suleiman ta kasance kabilar Nupe daga karamar hukumar Bida dake jahar Neja. Ta kammala digirinta na farko a harshen Turanci Wato English. Ta kasance daya daga cikin sabbin daliban da suka kammala digirinsu a wannan shekarar daga jami’ar IBBU LAPAI masu jiran wasikar kiran bautar kasa Wato NYSC.

A yayin da mujallar yanar gizon Gulmawuya ke tattaunawa da amaryar (Hauwa Suleiman) kan yadda ta hadu da angon na ta ce “Mun hadu ne a jami’ar IBBU Lapai a sashen kimiyya da fasaha na Jami’ar a lokacin ina daliba ina kokarin yin rajistar zango”.

A yayin da aka tambayeta game da na ta fahimtar game da shi (Ango Mohammed Nura Isah) a haduwarsu na farko ta ce “A farko dai bai burge ni ba saboda ya kasance mutum mai yawan son wasa da mata”

Amaryar wacce za ta amarce (Hauwa Suleiman) an tambaye ta da ta fadawa Gulmawuya abunda take so game da angonta (Mohammad Nura Isah) inda ta ce “Abunda ni ke so game da shi shine mutum ne mai gaskiya da rikon amana…”

Mujallar yanar gizon Gulmawuya ta tambaye amaryar da ta yi amfani da wasu yan kalamai kadai wajen bada karin haske game da angon na ta (Mohammad Nura Isah) inda ta fadawa Gulmawuya cewa “Namiji ne mai son kulawa da masoyiyarsa”.

Amaryar ta bamu wani rubutu da ta yi shi masoyin na ta na musamman domin nuna farin cikin da take yi da Allah ba ta angon irin Mohammad Nura Isah, ga rubutun a kasa; ku sani rubutun harshen turanci ta yi..

Shi angon Mohammed Nura Isah ya dan bamu damar lokacin tattaunawa da shi domin yi mana bayani a kan soyayyarsa da amaryarsa Hauwa Suleiman. Mun tambaye angon irin tambayoyin da mu ka yiwa amaryarsa a sama..

A lokacin da mu ka tambaye shi (Mohammed Nura Isah) da ya bamu labarin yadda suka fara haduwa da matar nasa (Hauwa Suleiman) ya ce “Na hadu da ita ne a sashen kimiyya da fasahar jami’ar IBBU Lapai wato ICT Centre a yayin da take ko karin rajistar zango na dalibai, a wannan lokacin na kasance shugaban wannan sashen.”

A lokacin da aka tambaye angon game da fahimtarsa na farko game da matar nasa a haduwarsu ta farko ya bayyana mana cewa “A haduwar mu ta farko gaskiya! a yanzu ba zan iya fadi ba amma sai dai abunda zan iya cewa shine ta kasance mace mai kyakkyawar hali”

Mujallar yanar gizon Gulmawuya ta tambaye angon da ya bayyanawa Duniya abunda ya fi so game da amaryarsa a nan ya ce “Ta kasance mace mai kulawa da kuma tausayi sosai a duk cikin matan da na yi soyayya da su a baya. Abunda na fi so da ita sosai shine ita ta sani na ki so na zama namiji gwarai a kodayaushe domin yadda ta ki nuna ma ni so”.

A lokacin da aka tambayi shi wannan angon da ya yi amfani da wasu ‘yan bayanai kadan game da masoyarsa ya ce “Itace madubin dubawa ta.”

Ku kalli hotunan gabanin auren wadannan masoyan a kasa;


Za a daura auren Nura da Hauwa da yardan Allah a ranar 26 ga watan Satumba, 2020 a layin Suleiman dake Chanchaga Minna, jahar Neja.

Ga katin gayyatansu a kasa;

Muna masu rokon Allah ya ba wadannan masoyan zaman lafiya bayan aurensu #amin….

Abun Kulawa: Kowa na iya zama amaren mu na mako ko wata, ga masu son zama ku tuntube mu a wannan lambar: 09065333995

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *