Abubuwa 3 Da Ke Sanadiyyar Warin Baki

Likitar hakora Shola Adeoye ta bayyana cewar sakamakon rashin kula ne da hakora ne ya ke kawo warin baki.


Likitar ta bayyana hakan ne yayin da take hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Ibadan.

Ta yi bayanin cewar mutane masu yawa su na fama da warin baki ne ba tare da sun san cewa bakin nasu na irin wannan warin ba, wanda kuma hakan ke sa wanda yake fama da cutar kasancewa cikin rashin jin dadi da walwala.

Adeoye ta kara jaddada cewa za a iya gane cewa ko baki na wari ne idan mutum ya lashi bayan hanunsa daga nan kuma sai ya sunsuna shi.

Har ila yau ta kara yin bayanin cewa idan da wari ya kamata mutun ya je asibiti domin a wanke masa ko mata domin samun lafiya dangane da ita cutar.

Bayan haka likitar ta ce da akwai wadansu hanyoyin da ke sa a kamu da irin wannan matsala ta warin baki da kuma suka hada da:

– Kamuwa da cutar dake kama makogwaro da kuma hanjin cikin mutum.

– Shan taba Sigari

– Bushewar baki.

Adeoye ta shawarci duk wanda ke fama da irin wannan matsalar ta cutar warin baki daya ya gaggauta zuwa asibiti domin a wanke masa hakora a kuma rika tsaftace baki da wanke harshe idan an zo wanke shi bakin.

By Idris Aliyu Daudawa

Share this:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *