Tarihin Bakin Dutsen Hajarul Aswad Wanda Ke Jikin Ka’aba


HAJARUL ASWAD Sunan wani dutse ne Baqi wanda ke manne ajikin dakin Ka’abah daga Kusurwar Kudu Maso gabas. Daga daidai inda yake, yana saitin rijiyar zamzam.

Wannan dutse mai daraja daga wajensa ne ake daukar niyyar fara Dawafi, kuma akansa ne ake Qarewa.

Shekaru dubunnai aru-aru, Daruruwan Annabawa (as) sun kama jikin wannan dutsen kuma sun sumbanceshi. Hakanan Annabinmu ma (saww) ya rikeshi ya sumbanceshi. Gaka Sahabbansa ma abayansa da Tabi’ai da Salihan bayin Allah da kuma Miliyoyin Musulmai masu zuwa aikin Hajji ko Umrah.

Ainahin Hajarul Aswad, dutse ne daga cikin duwatsun Aljannah, Allah Madaukakin Sarki ya sanya Mala’ikunsa suka kawoshi ga Annabi Aadam (as) ko Annabi Ibraheem (as).

Acikin Hadisin da Imamut Tirmidhiy ya ruwaito daga Sayyiduna Abdullahi ‘dan Abbas (ra) Manzon Allah (saww) yace:

“BAQIN DUTSEN NAN (HAJARUL ASWAD) YA SAUKO NE DAGA ALJANNAH KUMA YAFI MADARA FARI. AMMA ZUNUBAN ‘YAN ADAM NE YA MAIDASHI BAQI”.

Allah yana karbar duk addu’ar da aka yita awajen Hajarul Aswad. Kuma aranar Alqiyamah shi dutsen zai yi shaida mai kayau ga duk wadanda suka ta’ba sumbartarsa.

Manzon Allah (saww) yace “ARANAR ALQIYAMAH ALLAH ZAI BIJIRO DA HAJARUL ASWAD BISA WANI YANAYI WANDA YANA DA IDANUWA BIYU DA KUMA HARSHE. ZAI YI SHAIDAR IMANI GA WADANDA SUKA TA’BA SUMBARTARSA”.

(Imam Tirmidhiy ne ya ruwaitoshi).

Quraishawa sun ta’ba rushe Dakin Ka’abah sun mayar da gininsa. Amma wajen ‘Dora wannan dutsen bisa mazauninsa anan ne rigima ta kaure atsakaninsu. Suna jayayya akan shin wacce Qabila ce daga cikinsu wacce zata bada mutumin da zai dauki dutsen ya dorashi a bigirensa na ainahi??.

Zazzafan Yaqin basasa ya kusa barkewa atsakaninsu, har Banu Abdid Daar sun dauko wata Kwarya cike da jini kuma duk sauran Qabilun sun tsoma yatsunsu aciki (Wato alamar kowa ya yarda ayi Yaqin kenan). Sai Abu Umayyah Ibnul Mugheerah ya kawo wani hanzari.

Amatsayinsa na ‘daya daga cikin Shugabannin Quraishawa ya nemi amincewarsu akan cewa duk mutumin da ya fara shigowa haramin nan ta Kofar da ake kira QOFAR BANU SHAIBAH to su sanyashi amatsayin Alqali atsakaninsu. Sai kowa ya amince da haka.

Ana zaune kowa ya zuba ido ta wajen wannan Qofar, Sai ga Manzon Allah (saww) ya bullo ta wajen.. Sai suka ce “GA MUHAMMADUL AMEEN NAN (WATO AMINTACCE MAI GASKIYA). Alokacin nan shekarunsa talatin da biyar (35).

Bayan sun bashi labarin halin da ake ciki, sai ya shimfida Mayafinsa mai albarka, ya dauko dutsen ya dora bisa mayafin sannan yace musu kowacce ka Qabila ta sanya mutum guda daga cikinta yazo ya kama gefen mayafin.

Da suka kusanto jikin dakin sai shi kuma (Sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) ya sanya hannayensa masu daraja ya dauki dutsen ya dorashi amazaunin nasa.

Ta wannan hanyar ne Annabi (saww) ya kawo maslaha atsakanin Quraishawa awannan lokacin run kafin a aikoshi da Manzanci.

Abdullahi bn Abbas (ra) yace Watarana Manzon Allah (saww) ya jingina da dakin Ka’abah sai yace “HAJARUL ASWAD DA MAQAMU IBRAHEEM KAYAN ADO NE DAGA KAYAN ADON ALJANNAH. DA BA DON ALLAH YA ‘BOYE HASKENSU BA, DA SAI SUN HASKAKE DUKKAN ABINDA KE TSAKANIN MAHUDAR RANA DA MAFA’DARTA”.

(Imamut Tirmidhiy ne ya ruwaitoshi).

Lokacin Khalifancin Sayyiduna Umar (ra) an samu shigowar mutane da yawa cikin Musulunci har da Qabilun da ainahinsu suna bauta ma Duwatsu ne da bishiyoyi. To saboda kar suyi tsammanin cewa a Musulunci ma ana bauta ma duwatsu shi yasa Sayyiduna Umar (ra) da yazo sumbartar Hajarul Aswad yace ” NA SAN CEWA KAI DUTSE NE KUMA BAKA AMFANARWA KO CHUTARWA.. DA BA DON NAGA ANNABI (SAWW) YA SUMBANCEKA BA, DA BAN SUMBANCEKA BA”.

Acikin shekara ta 930 (Miladiyyah) wasu Mayaqan Qarmadiyyah mabiya Aqeedar Shi’ah Isma’iliyyah sun kawo hari garin Makkah. Sun kashe jama’a da dama, sun cika rijiyar Zamzam da gawawwakin Musulmai. kuma har sun dauke wannan dutsen sun tafi dashi zuwa garinsu mai suna IHSA’A a Qasar Bahrain.

Dutsen yayi shekaru 22 awajensu. Sai ashekarar 952 aka samu nasarar dawo dashi wajen da yake..

Ainahin dutsen a dunkule yake. Amma saboda abubuwan Yaqe-Yaqe da suka faru yanzu haka dutsen ya fashe zuwa gida takwas. Kuma suna kunshe ne acikin wani Murfin Azurfa.

Farkon wanda ya sanya ma dutsen nan Murfin Azurfa shine Sayyiduna Abdullahi bn Zubair bn Al-Awwam (ra). Kuma daga baya ma Khalifofin Banu Umayyah da na Banul Abbas sunci gaba da chanzawa.

Wasu Masanan tarihi sun ce akwai wasu bangorori guda shida daga jikin dutsen suna chan a birnin Istanbul na Qasar Turkiyyah. Amma dai bamu tabbatar da sahihancin hakan ba.

Kada jin wannan tarihin yasa ka rika tunkude mutane ko tattakasu domin samun sumbartar wannan dutsen. A’a in dai akwai chunkoso ba sai kaje har wajen dutsen ba. Idan ka nunashi da hannunka ko sandanka ma ya wadatar. Sai kayi kabbara yayin nunawar, Sannan ka sumbanci hannun ko sandan. Domin dukkan ukun Annabi (saww) yayi su.

Wato ya sumbanceshi. Ya nunashi da sanda, kuma ya nunashi da hannu ma.

AN GABATAR DA KARATUN NE A ZAUREN FIQHU

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *