Na Bata Rayuwata Na Shekara 15 Ina Bautawa Tafiyar Buhari, Inji Buba Galadima

Fitaccen dan siyasarnan na Nijeriya, Buba Galadima, ya bayyana cewa ya kwashe shekara sha biyar yana bauta a tafiyar shugaba Muhammadu Buhari. Ya bayyana hakan ne a a cikin Hirar da da ya yi da gidan rediyo da Talabijin na MADUBI a ranar Larabar 19 ga watan Agustan 2020 a cikin shirin MENE NE MAKOMAR NIJERIYA BAYAN MULKIN JANAR BUHARI? 

Buba Galadima ya ce; “na bata akasarin rayuwata na shekara goma sha biyar, ina bautawa tafiyar Janaral Muhammadu Buhari, da zaton cewa zai iya maganin abubuwa da yawan gaske da suka addabi kasarnan. Zai iya kuma daukowa Talaka kitse a wuta.”

Ya ci gaba da cewa; “da kuma karin cewa irin tashin-tashina da kuma rashin zaman lafiya da ake da shi a kasarnan, a matsayinsa na wanda ya taba zama shugaban Nijeriya. A matsayinsa na wanda ya taba zama kwamandan soja, a matsayinsa na wanda ya taba zama GOC, wato zai iya magance wadannan annoba da tashin-tashina a kasarnan, to ga shi ba haka aka so ba, kanin miji ya fi miji kyau. Sai muka tarar cewa ashe ma gwara mutumin da bai taba rike mukamin siyasa ba, a iya cewa ma, duk wani dan Nijeriya ya yadda cewa jiya ma ta fi yau.” Ya tabbatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *