Katsina: ‘Yan Bindiga Na Bada Gudummawa Sosai A Yawaitar Matsalar Fyade A Jihar – Masari

Gwamna Aminu Bello Masari na Katsina ya ayyukan ‘yan fashi da makami na bada gudummawa sosai a karuwar matsalar fyade a jihar.

Gwamna Masari ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya gabatar da jawabi a taron hadaddiyar kungiyar Kasuwanci (TUC) tare da hadin gwiwar kwamishiniyar mata wanda taron ya gudana a gidan Gwamnatin Katsina ranar Alhamis.

Gwamnan ya kuma nemi mata da su kasance cikin karfin hali wajen daukaka kararraki ga masu aikata laifin, domin su fuskanci hukuncin da doka ta tanada a kan su.

Masari ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar ta hannun majalisar dokokin jihar ta zartar da hukuncin kisa kan duk wanda a ka samu yayi fyade har ta kai ga mutuwa haka zalika wanda kuma ya aikata laifin fyaden ba tare da kisan kai ba to zai fuskanci hukuncin da ya dace.

Baya ga haka Gwamana Masari Ya yi takaicin cewa masu fyaden suna tsere wa adalci saboda mutane ba sa fitowa don ba da shaida a kansu.

Ya bayyana cewa a kwanan nan wasu matasa da suka rasa auran wata yarinya sai suka hada baki da a sace ta domin yi mata fyade.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *