Hukumar ‘Yan Sandan Yobe ta Gudanar Da Taron Tattaunar Yadda Za’a Inganta Tsaro A Jahar

Wakilinmu Muhammad Gambo Damaturu.

A kokarin sa na ganin cewa ya inganta sha’anin tsaro a jiha, Kwamishinan ‘Yansandan jihar Yobe CP Yahaya Sahabu Abubakar ya gudanar da wani taron tattauna harkar tsaro da shugabannin kananan cibiyoyin ‘Yansanda da na jami’an tsaron sa kai(Vigilante), maharba da sauran su.

Sanarwa, mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘Yansandan, ASP Dungus Abdul-Karim tace anyi taron ne ranar laraba 19 ga watan Agusta, 2020 a ofishin komishinan dake birnin Damaturu fadar mulkin jihar Yobe.

Sanarwar tace, anyi taron ne domin tattauna yadda za’a kawo karshen matsalar fyade, garkuwa da mutane, sace-sace, rashin jituwar manoma da makiyaya da dai sauran su a fadin jihar.

Kwamishinan ‘Yansandan jihar Yobe a cewar sanarwar, ya tunatar da jama’a cewa Gomnatin Yobe ta rantaba hannu akan dokar hukunta wadan da sukayi miyagun laifuka ta shekara ta 2020, kuma jami’an tsaro sun samu umarnin dabbaka dokar. Dokar ta tanadi babban hukunci ga duk wanda aka kama da laifin yin fyade, da sauran manyan laifuka.

Har ila yau, sanarwar tace, Kwamishinan ya wayar da kan jami’an tsaro na sa kai kan daukar aiki da hukumar ‘Yansanda take yi yanzu haka domin inganta sha’anin tsaro a tsakanin al’uma, wanda a cewar sa zai isar da tsaro duk wani lungu da sako na kasar ya kuma dakile miyagun ayyuka.

A bangare guda kuwa, membobin Kungiyar lauyoyi mata ta kasa da kasa wato (FIDA), sun kai wa Kwamishinan ‘Yansandan jihar Yoben ziyarar neman hadin gwuiwa domin kawo karshen matsalar fyade da nuna bambancin jinsi wanda yake kara ta’azzara a jihar Yobe.

Daga bisani kuwa, Kwamishinan ya ja hankulan su da sauran al’uman jihar da a hada kai da hukumar ‘Yansanda don samar da ingantaccen tsaro a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *