Gwamnati Tarayya Na Da Isassun Kuɗi Da Za Ta Biya Buƙatun ASUU- Sule Lamiɗo

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamiɗo ya ce Gwamnatin Tarayyar Najeriya tana da isassun kuɗin da za ta biya buƙatun Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya, ASUU, yana mai cewa jan ƙafa da gwamnatin ke yi a kan buƙatun na ASUU bai dace ba.

Idan dai ba a manta ba, ASUU ta tsunduma yajin aiki tun ranar 23 ga Maris, 2020, bisa rashin amincewa da sabon Tsarin Biyan Albashi na Bai Ɗaya, wato IPPIS da kuma wasu batutuwa da ba a aiwatar ba a Yarjejeniyar Aiki ta 2009 tsakaninta da Gwamnatin Tarayyar.

Mista Lamiɗo, dattijo a jam’iyyar PDP kuma tsohon ɗan takarar Shugaban Ƙasa ya bayyana wannan ra’ayi nasa ne a shafinsa na Twitter, inda ya ce ƙasar nan tana da isassun kuɗaɗe da za ta ceto ilimin jami’a daga durƙushewa.

A cewarsa, kuɗaɗen da Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, NCS ta tara, kuɗaɗen da aka gano daga Abacha da waɗanda Hukumar Hukunta Masu Yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati, EFFEC ta tara sun isa a biya buƙatun ASUU.

“Da biliyan N800 da Kwastam take tarawa duk wata, da kuɗin da aka gano daga Abacha, da waɗanda EFCC ta ƙwato, ina jin muna da isassun kuɗin da za mu biya buƙatun ASUU, don a ceto jami’o’inmu daga durƙushewa”, in ji Mista Lamiɗo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *