Dukar Rarara: Gaskiyar Abunda Ya Faru A Katsina (hotuna)

Tun jiya da yamma na ke samun kiraye-kirayen waya don ji gaskiyar lamari akan abun da ya faru na jifar Mawaki Dauda Kahutu Rarara, da su Ali Nuhu da ake ta yadawa a kafafen sadarwa na zamani.

Ko da yake, na samu yi wa wasu daga cikin su bayani a takaice, wasu kuma ban samu damar daukar wayar su ba sakamakon ayyuka da suka yi min yawa.

Ni ne mai taimakawa na musamman wurin samar da wuraren da aka yi aikin bidiyon wakokin da Rarara ya zo yin aikin su. Hakan yasa babu wani wuri da ba da ni aka je ba a lokacin aikin na su, barci kawai ke rabani da su.

Na ga an yi rubuce-rubuce na ri-ga malam Masallaci, kowane mai shafin yanar gizo da irin salon kanun labarin shi. Hakan yasa na ga ya dace da sanar da masu tambayata, da kum bibiyata ainahin abun da ya faru.

A ranar Laraba din ta gabata ne 19 ga watan nan na Agusta, Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya zo ya fara daukar bidiyon wakokin guda biyu da ya yi game da matsalar tsaro da ta ke addabar jihar Katsina. Wakokin su ne ‘Jihata, Jihata Ce, da kuma wakar ‘Masari Mai Hakuri’.

Wuraren da aka dauki wakokin sun hada da dakin taro na Local Government Service Commission da ke kusa da Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina. Sauran wuraren sun hada da Unguwar Kwado, kusa da masallacin dillali, akwai kuma Bakin kofar shigowa Katsina da ke Dandagoro, akwai kuma Gidan namun daji na ‘Al-Dusar’ da kuma bakin kasuwar Central Market Katsina daidai inda aka tada masu sayar da cefane, inda aka maida wurin ajiye motoci na masu shiga sayayya a kasuwar.

Inda ka cire dakin taro na Local Government Service Commission duk sauran wuraren da aka dauki wakar ni ne na samar da su, kuma ni na yi magana da masu kula da wurin.

Shi kan sa shugaban Kungiyar kasuwar ta Jihar Katsina, Alhaji Abbas Labaran Albaba, ni na kira shi ta waya tun da sanyin safiyar ranar Alhamis da misalin karfe 8:50am na safe, na sanar da shi abun da za mu zo yi a kasuwar, kuma na yi masa cikakken bayani, daga karshe ya yi mana fatan alheri.

A lokacin da ake aikin bidiyon wakar mai suna Jihata, Jihata Ce, wadda jarumi Ali Nuhu ke bada umarni, akalla an samu mutane sama da 500 wadanda suka zagaye mu suna kallon aikin. Duk kusan lokacin da za a dan dakata, Ali Nuhu da Rarara su kan koma mota domin sararawa, inda ‘yan jagaliya ke daddabe motar su suna neman a basu kudi.

Duk wadanda za su zo, Rarara ya kan basu daga naira dubu biyar abin da ya yi sama. Kafin a gama aikin wakar ya raba kudi sama da naira dubu dari. Sai ya gama da wasu, sai kuma wasu su zo, da kunnena na ji wadanda suka koma gefe suna kiran ‘yan uwan su ta waya, akan su zo su karbi rabon su a wurin na Kahutu.

Shi kuma da ya lura lamarin na su ba mai karewa ba ne, duk wadanda su ka zo, sai masu ya riga ya gama bada kudi, sai suce ai ba su yaba ba, su yanzu suka zo. Hakan yasa ya daina ba kowa kudi.

Wannan rabon kudin da ya daina, shi ya fusata wasu ‘yan jagaliyar wadanda ba su samu kudi ba, da wadanda suka zo daga baya, suka rika dabaibaye motar sa, har aka kammala aikin shi da Ali Nuhu lami-lafiya suka fita daga kasuwar suka koma masaukin su wato ‘Katsina Motel’ har saida masu gadin Rarara, su Tijjani Asase, Baba Ali, Scorpion, su ka ga sun fice daga wurin sannan su ka shiga mota suka tafi.

Bayan sun bar wurin, sauran ma’aikatan da aka zo da su, wadanda suka tsaya daukar Generator da sauran kayan aiki, ‘yan jagaliyar suka zagaye su suna cewa ” An dauko ‘yan iska da karuwai daga Kano an kwashe dukiyar jiha an basu”

Wadanda aka tafi aka bar su, sun hada da Furodusan wakar wato Abubakar Bashir Mai Shadda, Baballe Hayatu, Abubakar G. Boy, Kabiru Adebo, da sauran su, aka rika ce masu bamayi, karya ne. Har kuma mu ka bar wurin babu wanda aka fasawa gilashin mota, ko kuma danjar mota, kamar yadda wasu ke bada rahoton karya.

Daga jiya zuwa yau na ga mabambantan labarai a wasu shafukan Facebook da YouTube, kowa na rubuta abin da ran sa ke so ba tare da ya yi bincike ta kowane bangare ba, kamar yadda yake a tsarin aikin jarida ba. Sannan duka a cikin labaran ban ga inda aka tuntubi wani daga cikin masu ruwa da tsaki a aikin ba.

Abun da ya bani mamaki shi ne irin yadda na ga wasu suna tura labarin ba tare da sun samu sahihancin abun da ya faru ba. Wata tambaya da na ke da ita daga karshe ita ce, ace wurin da aka tara mutum sama da 500 kuma mafi yawancin su matasa, na san ba za a rasa akalla mutum 50 masu babbar waya, wadda za ta iya daukar bidiyo ba. Na ga mutane da dama, suna daukar bidiyon wakar, amma me ya sa ba a samu wadanda suka dauki bidiyon jifar ko kuma bugun kawo wukar da wasu ke rubutawa ba.

Har na gama bincikena a shafukan da su ka yi rubutun da kuma YouTube, ban ga bidiyon fasa gilassan motar su Rarara da aka ce an yi ba.

Dan Allah a jama’a a rika bincike na musamman kafin a rika yada labari, shi aikin Jarida ba aikin gaggawa ba ne, aiki ne da duk wanda ya ke yin shi, ake ma shi kallon mutum mai hankali.

Daga Isah Bawa Doro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *