Dalilin haifar jarirai da shanyayyen hannu

Daga cikin matsalolin da jarirai kan fuskanta yayin haihuwa da kan sanya a haife su da shanyayyen hannu akwai larurar nan da ake cewa “Obstetric Erb’s Palsy” a turancin likita. Wannan matsala tana faruwa ne sakamakon raunata tushen jijiyoyin laka ta biyar da ta shida daga cikin jijiyoyin laka da suka fito daga wuya sannan suka sauko zuwa hannu domin kai saƙonnin ƙwaƙwalwa.

Haɗarin raunata waɗannan jijiyoyin laka yayin haihuwa na da alaƙa da:

1) Tankarewar kai ko kafaɗar jariri a ƙugun uwa yayin haihuwa; wannan zai sa a ɗame jijiyoyin lakar tsakanin wuya da kafaɗa.

2) Rashin ƙwarewar ungozoma wajen janyo kan jariri yayin temaka wa mai haihuwa.

Gwargwadon girman raunin da aka yi wa jijiyar lakar gwargwadon girman nakasun da hannu zai samu.

Saboda haka, jijiyar lakar za ta iya samun rauni ta hanyar:

a) Ɗamewa

b) Yagewa

c) Tsinkewa ko cisgewar tushenta daga jikin laka.

Alamomin wannan larura:

Kamar yadda aka sani, duk lafiyayyen jariri kan kasance cikin mommotsa ƙafafu da hannaye a kowanne lokaci. Sai dai, duk jariri mai wannan larura zai kasa iya lanƙwasa ko ɗaga hannu kamar yadda yake yi da ɗaya hannun. Wannan matsala za ta iya kasancewa a hannun hagu ko dama, wani lokacin ma duka hannaye biyun.

Ɓarin da yake da wannan matsala zai kasance:

1) Hannu a ɗanfare da jiki.

2) Hannu ya murɗe / juye ciki.

3) Gwiwar hannu a miƙe.

4) Yatsun hannun a dunƙule.

Ga duk jijiyar lakar da ta ɗame ko ta yage aikinta na kaiwa da komowar saƙonni zuwa tsokokin hannu zai samu cikas. Amma yayin da jijiyar laka ta tsinke to aikinta zai yanke ne gaba ɗaya.

Likitocin fisiyo ne ke da alhakin farfaɗo da ayyukan jijiyoyin laka da tsokokin da suka sami wannan matsala.

A tuntuɓi likitocin fisiyo da zarar an lura da jariri ko yaro ba ya iya amfani da ɗaya daga cikin hannayensa yadda ya kamata bayan haihuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *