Yadda Ake Koran Tsaka Da Kenkeso A Gida

Duba da hatsurran dake tattareda wadannan halittun guda biyu,sai muka ga ya dace mu zo da bayanin tiryan tiryan kan yanda ake korar tsaka da kenkeso ga baki daya a cikin gida.
Ta’ammali da tsaka a cikin gida masifa ce,mun yi rubutu kan dimbin illolin da take haifarwa a gida,ko baya ga haka halitta ce munafuka da addinin musulunci yaiyi umurnin idan an ganta a kashe ta.Akoi lada ga Wanda ya aikata haka.
Shi kuma kenkeso yana dauko kwayoyin cuta daga najasa a toilet ya zo ya cudanyasu ga abinci,ruwan sha,ko abin shan da aka ajiye.
Halitta ce da take da tsawon rayuwa zata iya daukar shekara da shekarru tana rayuwa a bayi,tana haddasa cutukan polio,cholera, typhoid,da matsanancin basir,da gudawa marar misali.
Duk abinci ko wani abin shan da ta fada a cikinsa to ka zubda wannan abin kada ka kuskura ka ci ko ka sha,wallahi hatsari ne ga lafiya matuka.
Domin korar tsaka a gida,ka nemi gishiri ka gauraya da garin tafarnuwa sai ka marmasa a kowace korkoda a gidanka,tsaka zata bar wajen a cikin gaugawa.
Shi kuma kenkeso,ka nemi albasa guda daya,da cokali daya na baking soda (sodium biocarbonate) bafa baking powder ba,sai a kula.
Sai ka yayyanka albasara ka gauraya da baking soda din ka ajiye a korkodar kitchen ko a toilet, zaka ga yanda kenkesai zasu mutu.