Zai Yi Wuya Na Iya Rufe Duka Jikina, Saboda Kyawu Na Ba Zai Boyu Ba, Inji Jaruma Fati S.U Garba.

To me yasa ma zan boye kyakyawar halittar da Allah yayi min ita kyauta ?

-Ba zan taba wucewa ta gaban maza ba, har sai sun kalleni sau biyu.

Daga:

Shehu Rahinat N’Allah

Jaruma a masana’antar Kannywood Fati S. U. Garba wacce ‘yar asalin jihar Naija ce tayi karatun ta na HND a Business administration a Federal Polytechinc Bida inda tayi NYSC dinta a Kaduna.

A wata hira da jaridar Blueprint tayi da ita, Jarumar a masana’antar Kannywood ta bayyana wa duniya cewa tana fatar Allah ya bata miji na gari tayi aure, amma idan so samu ne ya zama dogo ne kyakyawa wanda zata iya nunashi ko ina a matsayin mijin ta.

Da ake mata tambaya akan ko zata iya auren mai mata uku Jarumar tace: To mai zai hana! Duk da dai babu dadi ace kuna sharing namiji da wata mace, amma tunda addinin mu ya bada dama to wacece Fati S.U. da zata canja dokar Allah, amma dai nafi so na zama nice ta farko.

Da ake tambayar ta ko ta taba yin soyayya ?
Jarumar tace eh! ta taba yi, ta sanadin hakan ne ma yasa ta iya bambance masoyin gaskiya da kuma na karya.

Hakanan da Jaridar ta kara tambayar ta akan yanayin saka kayan da tayi mai nuna surar jikinta gaba da baya a cikin wani Film mai suna THIS IS THE WAY

Jarumar tace: Na gode Allah da ya yini kyakyawar budurwa ! tabbas ina da mama (Boobs), kuma ina da mazaunai (Hips). Amma inaso mutane su sani akwai bambanci tsakanin rayuwar Film da kuma ta hakika. A film muna yin abunda aka bamu ne a rubuce.

Amma a rayuwa ta gaskiya ba film ba, amatsayi na na mace musulma ina sanya sutura na ne kamar yadda ya dace, amma da akwai wahala na iya rufe duka jikina, saboda kyawu na ba zai boyu ba. To me yasa ma zan boye kyakyawar halittar da Allah yayi min ita kyauta ?

Har ila yau dai an tambayi jarumar akan ko zata iya auren NUHU ABDULLAHI wanda ya fito matsayin saurayin ta a cikin film din mai suna THIS IS THE WAY ?
Jarumar ta amsa da cewa: Ina mai tabbatar maka da cewa ma yana daga cikin jaruman da nafi so.

A zahirance ba a film ba, idan Jarumi Nuhu Abdullahi yace yana sona zan aure shi, to me yasa ma bazan aure shi ba ? Mutum ne mai ilimi da hazaka, gashi kuma Jarumi ne kyakyawa. Amma hakan da na fada fa ba wai yana nufin ina shirin yin haka bane, a’a kawai dai abokin aiki na ne, kuma abokina ne sosai, babu wani abu sama da haka.

A karshe an tambayi Jarumar dangane da lokutan da bataji dadin su ba.

Jarumar tace a gaskiya ba suda yawa. Na farko dai ni Graduate ce, na biyu ba zan taba wucewa ta gaban maza ba har sai sun kalleni sau biyu, na uku kuma ni musulma ce, sabida haka bana wani da na sani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *