‘Yan Sanda Sun Kama Wasu Matasa 3 ‘Yan Tsakanin Shekaru 13 Zuwa 16 Kan Laifin Aikata Fyade

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu matasa uku a garin Dan Musa dake Jihar Katsina, bisa zargin aikata fyade da kisan Kai.

Lamarin dai a faru ne a garin Dan Musa dake jihar Katsina, inda matasan uku masu shekaru 13 zuwa 16 suka yi wa yarinyar mai shekaru 13 fyade, daga bisani suka kasheta suka jefa gawarta cikin kogi.

Tun farko dai matasan uku da suka hada da Mubarak Lawan da Anas Ibrahim da kuma Aliyu Mika, suna aiki a gonarsu dake garin Dan Musa, suka hango ‘yan mata da zarga da yi musu satar leman tsami.

Bayan da suka tunkari ‘yan matan ne sai suka gudu suka bar yarinyar mai suna Safiya Basiru a baya, matasan sun rike ta tare da cire mata kaya, sannan dukkanninsu su ka kwanta da ita daya bayan daya.

Daga karshe yarinyar na ta faman ihu sai Aliyu Mika ya dauki Yashi ya cika ma ta baki domin ta yi shiru. Bayan ya kashe ta ya jefa gawar cikin kogi.

Allah yakyauta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *