Kar Ka Kuskura Ka Kara Tsoma Mana Baki A Cikin Harkokin Cikin Gidan Mu – Cewar Shugaban Kasar Mali Ga Buhari

Shugaban kasar Mali kanal sadio camara ya gargadi shugaban kasar Nigeria muhammadu Buhari akan kada yakara tsoma musu baki a cikin harkokin su Na cikin gida.

Kanal sadio camara yace kasar Mali ba kasar Nigeria bace, kasar Mali daban kasar Nigeria daban, don haka su sukasan mawuyacin halin dayasa suka hambarar da gwamnatin farar hula a kasar su.

Kanal sadio camara yakara da cewa basuyi juyin mulki a kasar su ta Mali ba seda suka samu tabbacin goyon bayan talakawan kasar su ta Mali Wanda hakan ne ya tabbatar musu da cewa talakawan kasar Mali sun gaji da mulkin tsohon shugaban kasar Mali bubacar kaita, basajin dadin mulkin.

Kanal sadio camara yace don haka shugaban kasar Nigeria muhammadu Buhari yaguji tsoma baki a cikin al amuran da bashi da hakikannin sanin gaskiyar abinda yake boye.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *