Kungiyar Miyetti Allah Ta Kaiwa Hukumar Bada Agajin Gaggawa Ziyara


Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta jihar Jigawa ta kai ziyara ga hukumar bada agajin gaggawa ta jiha wato SEMA.


A jawabinsa shugaban kungiyar, Umaru Kabiru Dubantu Hadejia ya ce sun kai ziyara hukumar ne domin yabawa hukumar dangane da ayyukan bada tallafin da take yi a fadin jihar nan, inda ya yi kira ga hukumar data rika tallafawa Fulani aduk lokacin da iftilai ya same su.

Shi ma a jawabinsa shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jiha, ya yabawa shugaban kungiyar dangane da ziyarar da suka kawo masa, inda ya basu tabbacin tallafawa Fulani kamar yadda hukumar take aiwatarwa a duk lokacin da iftilai ya same su.


Ya kuma yi kira ga kungiyar data rika rubuto takadda domin sanarwa hukumar a lokacin da wani iftila`i ya faru wanda ke bukatar tallafin hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *