Hukumar Jin Dadin Alhazai Ta Jahar Jigawa Ta Mayarwa Maniyyatan Aikin Hajjin Bara 178 Kudadensu


Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Jigawa ta mayarwa da maniyatan aikin hajjin bana 178 kudaden su na ajiya kimanin naira miliyan dari biyu


Shugaban kwamitin tantance maniyatan dake bukatar mayar musu da kudaden aikin hajjin bana da wadanda suke san ajiyewa zuwa shekara mai zuwa na hukumar Alhaji Ahmad Umar Labbo ya sanar da hakan a wata sanarwa, inda yace maniyatan aikin hajjin bana 558 ne suka biya kudadensu na ajiya a hukumar


Yace kwamitin zai yi rangadin shiyoyin hukumar daga mako mai zuwa domin tantancewa da kuma tabbatar da cewar an biya masu san a basu kudadensu na ajiya da kuma masu san su ajiye kudaden zuwa aikin hajjin badi


Alhaji Ahmad Umar Labbo wanda kuma shine daraktan aiyukan na hukumar yace zasu fara rangadin ne a ranar talata daga ofishin shiyyar hukumar na Kazaure da Gumel wadda ta kunshi kananan hukumomin Kazaure da Roni da Gumel da Maigatari sai ranar laraba da zasu ziyarci ofishin shiyya na Hadejia daya kunshi kananan hukumomin Hadejia da Kirikasamma da Kafin Hausa da Kaugama da Ringim sai ranar 25 ga wata da zaasu ziyarci ofishin shiyya na Dutse daya kunshi kananan hukumomin Dutse da Birnin kudu da Gwaram da Jahun. Sanarwar ta bukaci shugabannin shiyyar dasu hallara a wuraren tantancewar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *