Yara Miliyan 46 Aka Tursasa Musu Ficewa Daga Makaranta Sakamakon Cutar Korona – Hukumar NITDA


Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa ta ce yara yan makarantu miliyan arbain da shida ne aka tursasa musu ficewa daga makarantu sakamakon annobar korona a kasar nan.
Babban Daraktan hukumar, Malam Kashifu Abdullahi Inuwa ya bayyana haka ga taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a Abuja.


Ya lura cewa ya zuwa yanzu dalibai dubu ashirin da hudu da dari uku da saba`in da biyu ne da suke karatu a makarantar dake karkashin Hukumar ta kafar sadarwa ta zamani domin kara inganta ilimin su daga gida sakamakon barkewar cutar korona.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *