Jigawa: Hukumar Shige Da Fice Ta Dauki Alkawarin Magance Zirga-Zirgar Rakuma A Bisa Kan Manyan Hanyoyi


Hukumar shige da fice ta kasa a jihar Jigawa tayi alkawarin daukar matakan magance zirga-zirgar rakuma akan manyan hanyoyin jihar nan lamarin dake haddasa hadduran mota akan hanyoyin.
Kwanturolan hukumar, Ismaila Abba Ali ya bada wanann tabbacin lokacin da ya ziyarci karamar hukumar Maigatari a cigaba da rangadin kananan hukumomin jihar nan. Yace hukumarsa da hadin gwaiwar sauran hukumomi zasu dauki matakan dakile matsalar domin magance afkuwar haddura.

Haka kuma Ismaila Abba Ali yayi alkawarin ganin dukanin kananan hukumomn jihar nan suna samun kasonsu wajen daukar maaikata a hukumar. Kwanturolan wanda yayi kira ga baki yankasashen waje mazauna jihar nan suyi rijista da hukumarsa, yace yanzu haka ana cigaba da bada fasfo ga masu tafiya kasashen waje wanda aka dakatar a kwanakin baya sakamakon cutar Korona.


A nasa jawabin shugaban karamar hukuamr, Maigatari, Alhaji Sani Dahiru wanda ya sami wakilcin shugaban majalisar kansilolin yankin, Alhaji Ibrahim Adamu ya bada tabbacin hadin kai ga hukumar domin ta samu nasarar gudanar da ayyukanta.


Haka kuma kwantirolan ya ziyarci iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijer dake Maigatari da kuma fadar Hakimin Maigatari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *