Gwamnatin Tarayya Na Alfahari Da Gwamnan shigar Jigawa Badaru – Ministar Noma


Ministan aikin gona na kasa alhaji sabo na nanono yace gwamnatin tarayya na alfahari da gwamna Muhammadu Badaru Abubakar bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen bunkasa aikin gona a kasar nan.


Alhaji sabo nanono ya baiyana haka a lokacin bikin kaddamar da dashen itatuwa a garin kaya na karamar hukumar garki.


Alhaji sabo nanono yace gwamna Muhammadu Badaru Abubakar yana daya daga cikin jigajigan dake tallafawa gwamnatin tarayya wajen tsarawa da kuma aiwatarwa da manufofi da tsare-tsaren aikin gona a kasar nan.


Yace koda a jihar jigawa sun sheda irin sauyin da gwamna ya kawo a fannin tattalin arziki da kuma samar da aikin yi a tsakanin alummar jihar nan.
Daga nan Ministan ya bukaci alummar jihar nan su tallafawa kudirin gwamnatin tarayya baya na inganta noma domin bunkasa samar da abinci.


A nasa jawabin gwamna Muhammad Badaru Abubakar yace tuni gwamnatin jiha tayi nisa wajen zabar wasu rukunin bishiyoyi domin yaki da kwararowar Hamada da kuma zaizayar kasa
Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya bisa gudunmawar da take baiwa jihar jigawa a duk wani lamarin da ya shafi kyautata rayuwar alumma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *