Ba Za Mu Zura Ido Ana Tunzura Al’umma Ba -DSS Ga ‘Yan Nijeriya

Hukumar tsaron kasa ta farin kaya, DSS, ta gargadi ‘yan Nijeriya akan su yi hattara da yada kalaman da za su yi iya rusa doka da oda da kawo hargitsi a kasa.

Hukumar ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a ta hannun Kakakinta, Dakta Peter Afunanya cikin wata sanarwa da suka fitar a birnin tarayya Abuja.

Ya tabbatar da cewa hukumar a ranar 27 ga watan Yuni, ta ankarar da ‘yan Nijeriya kan kokarin da wasu fitattun mutane suke yi na cimma wata boyayyiyar manufa ta hanyar amfani da tasirinsu a cewarsa.

Dr Afunanya ya ce hukumar DSS ta bayyana cewa daga cikin ayyukan da suke yi akwai ingiza wasu gungun jama’a kan wasu a cikin a cikin kasarnan domin tada hankali. Afunanya ya ce idan aka yi la’akari da abubuwan da yake faruwa a kasarnan, to ‘yan Nijeriya ba su da hujjar karyata batun DSS din.

DSS din sun kawo batun da tsohon mataimakin gwamnan Bankin Nijeriya, CBN, Mailafiya ya yi na cewa akwai wani gwamna a arewa wanda Kwamandan Boko Haram ne. DSS sun ce Mailafiya mutum ne da ya san duk hanyoyin da ake bi na ganin jami’an gwamnati. “Amma abin takaici sai ya zabi ya tsallake iyakarsa,” inji shi.

Ya ce zantukan Mailafiya sun nuna kawai yana son ya yi amfani da labaran karya ne wajen tunzura mabiyansa. Inda ya nuna takaicinsa na yadda bai taba wani yunkurin sanar da jami’an tsaro abubuwan da ya sani ba.

“Abin takaici da Allah-wadai ma shi ne yadda Mailafiya duk da hakuri da ya rika bayarwa a lokacin da ziyarci ofishin DSS a Filato kan kalaman na shi, sai ya juya kuma ya sanar da duniya cewa yana nan a kan bakarsa”. Inji shi.

Hukumar ta ce ba za ta zura ido ta rika ganin wasu suna ingiza jama’a wajen daukar doka a hannunsu ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *