‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Garin Mariga Jahar Neja (hotuna)

Al’amarin tabarbarewar harkar tsaro na cigaba da ƙamari a ƙauyukan ƙaramar hukumar Mariga dake Jihar Neja. Hotunan gawarwakin bayin Allah kenan da barayi suka kashe a garin Ukuru a shekaran jiya a lokacin da ake shirin yi masu sallar jana’iza.

Wannan al’amari kamar wasa kullum abun sai daɗa faɗaɗa yake yi. Wanda yanzu kusan ba ƙauyen dake ƙaramar hukumar Mariga dake kwana cikin kwanciyar hankali.

Maigirma gwamnan Jihar Neja ya sani haƙƙin kare ran waɗannan bayin Allah yana a yuwar sa, muna buƙatar mu ga ya ɗauki matakin gaggawa akan wannan al’amari domin ganin talakawan wannan yanki sun samu zaman lafiya da salama.

Aƙarshe muna roƙon Allah ya tona asirin duk wanda keda hannu a wannan aika aika dake faruwa a Arewa. Allah ya kawo mana ƙarshen wannan mafisa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *