Turakan Zamantakewar Aure

Tushen Aure (2)

A makon da ya gabata, mun kawo kaso na farko na wannan batu mai girma, wato jigogi ko dalilan da tun farko ake kulla auratayya bisa doronsu, bisa la’akari da nassi daga al kur’kni mai girma. Wanda mun dauki gaba ta farko (nutsuwa) mun dan tattauna a bisa halin gajertawa game da ita. A wannan makon kuma muke shirin tsallakawa ga matakai na gaba, da yaradar Aallahu.

(b) Tausayi

Ina tuna wani Karin Magana da tsofaffi kan yi cewa: “Dadi musaya ne, ko da mahaifiyarka ne.” Ma’ana, yin wani abu sawa’un magana ce ko aiki ko kyuata, wanda zai sa wani ya ji dadi idan an yi masa, to tamkar musayan sa ake yi. Domin kowane dan’adam yana yawaita yin wannan abin (da zai sa wani ya ji dadi ne) ga wanda yake yi masa. Kenan idan ka zama ba ruwanka da yi wa mutum abin da zai faranta masa rai, shi ma a hankali ko yana yi maka zai gaji, abin duk ya ji ya gundire shi, ya dena. To wannan kuma shi ne abin da yake faruwa cikin ayyukan da ake gudanarwa tsakanin ma’aurata, wanda a cikinsu har da tausayi ga juna. Kodayake, bayan musayar tausayin da ake yi, akwai kuma aiki ko ayyukan da mutum ya kamata ya yi kafin a yarda ya cancanci a tausaya masa din. Haka nan, a hannu guda akwai abin da mutum zai yi wanda zai hana a ji tausayinsan, ko da kuwa ya shiga hali ko yanayin tausayi din.

Yayin da duk kake son mutum ya tausaya maka, to fa dole sai ka siffantu da abin tausayi din. Domin tausayi ana iya kaddara abubuwan da suke haifar da shi ta sigogi biyu, manya. Ko dai tausayi ya zama irin wannan. Wanda ake musayarsa, wato ka ji kawai wani ya damu da kai, yana ta yin wasu ayyuka ko maganganu ko mikowa, don kawai ya rage maka radadi ko ya kara maka karsashi ko ma ya faranta maka rai, sai ka ji tabbas babu ya shi, kuma har ma ka ji kana tausayinsa. A wannan karon ba don rauninsa ba, a’a, don dawainiyar da yake ta faman yi da kai, komai karfi ko arzikinsa kuwa.

A hannu guda kuma, tausayi, shi ne bude ido da kyua ka kalli bangaren da abokin zamanka yake da rauni, kuma ka yi masa uzuri a cikin gazawarsa ta wannan fannin. Misali, dukkanmu mun yarda mata ba su da karfin damtse kamar maza, saboda haka ba za su iya yin ayyukan karfi kamar yadda maza suke yi ba. Haka nan, watakila mun san karfin zuciyarsu da dakewa ma ba su kai na maza ba. Don haka abin da zai ba su tsoro, ba lallai ne a wurin maza ya zama abin tsoro ba. Harwayau, aikin da namiji zai iya yi ma karfi, su ma ba lallai ne su gwada yn shi ba.

To yayin da duk ka ga an zo wani abu da matarka ta kasa, kamata ya yi kai kuma nan take sai tausayinta ya kama ka. Maimakon ka hau ta da fada, ko ka fara murtuke fuska. Ita ma mace dole ta sani cewa ba wai komai ne ake yi da karfi ko dagiya ba. Wani aikin na matan ne, kuma ba lallai mazan su iya ba. Wani aikin kuma namijin ba zai iya ba sai ya samu karfafar gwiwa daga matar tasa. Yayin da a wani lokacin kuma, so yake kawai matar tasa ta fahimci yanayin da yake ciki na gazawa, watakila wurin biyan bukatarta ta karan kanta, ko ta iyali daukacinsu. Wadda a irin wannan lokaci babu abin da zai iya kwantar wa da magidanci hankali kamar samun fahimta da tausasawa daga iyali. Don haka a cikin irin wannan yanayi dole a tausasa wa maigida.

Dole ma’aurata su yarda cewa ayyukansu sun sha bambam. Akwai abin da mace za ta iya, amma namijin ba zai iya ba. kamar yadda wasu abubuwan da yake yi ita ma ba ta iya su.

To yi wa juna uzuri a irin wadannan wurare, yana da cikin samfurin ainishin tausayin da ya kamata a ce ma’aurata suna samarwa a junansu.

Shi ne kwanaki na ke buga misali cewa, idan kana da yara guda uku. Kuna cikin tafiya aka zo tsallaka wata katuwar kwata. Kowanne daga ciki ya tsalle, ya tsallaka. Amma sai babbansu ya tsaya, yana kuka, wai shi ba zai iya ba, sai an taimaka masa. Nan take sai ka ji ranka ya baci. Saboda ya za a yi yara su yi abu shi kuma babbansu ya kasa?

To amma daga baya sai ka kara kallon kafarsa, sannan ka tuna ashe fa shi gurgu ne. A wannan lokaci babu abin da zai cika zuciyarka sai tausayinsa. Domin ka tabbata shi ma hakan ba a son ransa ba ne, in a son sa ne ya fi son ya taimaki wasu ma, ba wai shi ya zama sai an taimmaka masa ba.

To kamar haka ne kuma ya kamata magidanta su rika kallon abokan zamansu a cikin fannonin da suka nuna gazawa. Su tsaya su dubi damuwar, kuma su tausaya. Magidanta a nan ban a nufin maza kawai.

Haka nan, a tausaya wa abokan zama yayin sake su ayyuka. Kar a rika yawaita ba su aiki. Kuma idan aikin ya zama dole, to a tausaya musu, ta hanyar taya su aikin. Kamar yadda aka samu daga Anas bn Malik (r.a) ya na cewa “Annabi Sallallahu alaihi wa sallam ya kasance cikin hidimtawa iyalinsa. (idan ya na cikin gida).”

Idan Annabi SAW ya taya iyalinsa ayyukan cikin gida, to kuma wane ni wane kai, su wane ku, da ba za mu taya namu iyalan ba?

Su ma mata, kodayake su da ma sun fi yi. Akwai bukatar su kara kaimi wurin taya mazajensu ayyuka. Kamar wanke kayansa, gogewa, da sauransu, yayin da shi kuwa watakila ya tafi nemo mu ku abinci.

Wannan yana daga cikin manyan alamomin nuna tausayi da jin-kai a tsakanin ma’aurata.

Kodayake, yana da kyau mata su sani cewa wadannan ayyukan da suke yawan taya maza, ba za su taba taimakawa ba in dai har ba su samu nutsuwa a ransu ba. Abin nufi shi ne, mafi girman taimakon da mace za ta iya yi wa namiji a matsayinsa na mijinta shi ne ta samar da wani yanayi a zuciyarsa wanda zai rika jin cikakkiyar nutsuwa da ita, ta kowane fanni. Wato ya zama ba ya jin tsoron komai game da ita.

Ba ya tsoron ta a cikin kayayyakin.

By Muhammad Baqeer aure

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *