Yadda Mata Ke Neman Yin Madigo Da Ni – Inji Jarumar Fim

Wata tauraruwar fim daga kudancin Najeriya wadda ta kware a fagen Barkwanci me suna Ada Ebere ta bayyana cewa mata ‘yan uwanta ‘yan Fim na matukar kawo mata harin neman su yi madigo da ita.

Ta bayyana cewa manyan nonuwan da Allah ya bata ne yasa data fita waje koda mutanen gari kamin su kalli fuskarta, sai sun kalli kirjinta.

Tace wani karin abin damuwa shine bata iya gudu sai ta rike nonuwan nata hakanan bata iya kwanciya ruf da ciki saidai ta yi rigingine ko kuma ta kwanta a gefe.

Tace hakanan bata iya samun rigar mama daidai ita saidai ta siya ta gyara sannan kuma wasu lokutan da damama bata saka rigar maman hakanan take fita.

Ta bayyanawa Inside Nollywood wasu ma na tunanin wani magani tasha nonuwan nata suka yi girma haka amma maganar gaskiya daga Allah ne.

Tace bata son manyan Nonuwa ta fi son madaidai ta amma tunda Allah ya bata, tana godiya, daisai tace nan gaba zata je a mata aiki dan kara girman mazaunanta.

Ta kara da cewa kuma yawancin neman yin lalata da ita da take samu daga wajan Mata ne ba maza ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *