Tun A Baya Ina Da Arziki Na Kamin Ka Bani Mukamin Ministan Shari’a Abubakar Malami Ya Gayawa Shugaba Buhari

Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya bayyanawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa dama can shi me kudi ne tun kamin shugaban kasar ya bashi mukamin Minista.

Malamai ya aikewa da shugaban kasa wannan bayanine saboda yanda wasu ke ta kira a tuhumeshi kan Almundahanar Miliyoyin Kudi.

A cikin takardar bayanin da ya aikewa shugaban kasar, Malami ya bayyana cewa cikin bayanan da ya bayar kamin ya zama Minista ya saka kadarori 27 da ya mallaka.

Daga Comr Yaseer Alhassan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *