Shekau Ya Yiwa Zulum Barazana A Wata Sabuwar Bidiyo Da Ya Sake

Shugaban kungiyar Boko Haram,  Abubakar Shekau ya saki Sabon Bidiyo inda yawa gwamna Babagana Umara Zulum da tsohon Gwamnan Borni, Kashim Shattima da me baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Babagana Mungono da kuma Lauya, Bulama Bukarti barazana.

A bidiyon wanda Daily Nigerian ta samo an ji Shekau ya fassara taken Najeriya dana Dalibai masu hidimtawa kasa inda yace duk wanda ya karanta wannan take to ba musulmi bane koda yana sallah yana Azumi kuwa dan haka yace ya jinin musulman Najeriya ya halatta.

Ya kira sunan gwamna Zulum da Kashim Shattima inda yace su yi hankali kuma tafiyar da yake ba takalmi ba zata taimakeshi ba.

Yace idan dai suna karanta taken Najeriya da na matasa ‘yan Bautar kasa ko da da wasane sun kafirta.

Ya bayyana cewa, Bulama Bukarti da tsohon ministan matasa da Wasanni, Solomon Dalung su sani tasu ta kare.

Saidai Bukarti ya mayarwa da kungiyar Martani inda yace barazanatsu ba zata sa ya daina yaki da manufofin kungiyarba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *