Soja da ta yi ciki bayan ƴan bindiga sun mata fyade ta daukaka kara

Wata soja da rundunar sojojin Najeriya ta kora daga aiki saboda ta samu juna biyu bayan wasu da ake zargin yan bindiga ne sun mata fyade a hanyarta na zuwa Ogbomosho a jihar Oyo ta daukaka kara.

An tuhumi matar ne da aikata laifi daya na rashin da’a kuma aka kore ta daga aiki bayan kwamitin binciken da rundunar soji ta kafa, (BOI) ya same ta da laifi kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Lauyan sojan, Johnson Oyewole ya ce korar wacce ya ke karewar ya saba wa doka kuma ya bukaci shugaban hafsin sojojin kasa, Laftanat Janar Tukur Buratai ya soke hukuncin korar.

Soja da ta yi ciki bayan yan bindiga sun mata fyade ta daukaka kara kan korarta daga aiki. Hoto daga The Punch Source: Twitter Takardar daukaka karar ya nuna cewa wacce abin ya faru da ita ta shiga aikin soja ne a watan Maris na 2012 a 67 Regular Recruits intake kuma tana aiki da 56 Signal Command, Mile 2 a Legas kafin abin ya faru.

Barrista Oyewole ya ce; “Bisa ga dukkan alamu akwai matsaloli da dama tattare da shariar da aka yi wa wanda muke kare wa, babu inda dokar aikin ya yi maganar daukan ciki a lokacin aiki laifi ne da ya dace a kori mutum saboda ita karkashin sashi na 103 (1).”

Ya kuma bayyana cewa wacce ya ke kare wa ta nemi izinin yin tafiya zuwa jihar Oyo a watan Oktoban 2014 a inda yan bindiga suka tare mitar da ta shiga a hanyar Odo Oba kuma wasu mutum biyar suka yi mata fyade.

An kai ta asibitin Jamiar Fasaha ta Ladoke Akintola da ke Ogbomosho inda ta yi kwanaki shida ana mata magani. An kuma gano cewa sojar ta gabatar da rahoton karar da ta shigar a ofishin yan sanda, rantsuwar kotu, da rahoton likita da ke nuna cewa ta samu rauni a gwiwa da cinyar ta.

A watan Disamba ne ta tafi asibitin sojoji ta koka kan cewa bata da lafiya kuma aka tabbatar tana dauke da cikin makonni 12. Vanguard ta ruwaito cewa daya daga cikin manyan dalilan da yasa aka kori sojar daga aiki shine tsawon lokacin da ta dauka daga ranar da abin ya faru da kuma zuwan ta asibitin sojojin inda aka tabbatar tana dauke da juna biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *