Shugaban Majalisar Dattijai Ya Jajanta Mutuwar Ladan Ayawa Tsohon Ma’aikacin VOA

Shugaban majalisar dattijai ta qasa, Ahmad Lawan ya bayyana alhininsa kan mutuwar Malam Ladan Ayawa tsohon ma’aikacin muryar amurka.

Lawan ya bayyana hakan ne a wata takardar sanarwa ga manema labarai ta hannun mai taimaka masa akan harkokin labarai, Malam Babangida Jibrin juma’ar makon nan mai qarewa. Inda ya jajantawa iyalan mamacin akan wannan babban rashin.

” Mamacin ya tava vangarorin rayuwar jama’a wanda ya kawo cigaba ta hanyar aikin jarida ga al’umma a Najeriya wanda yake da kyakkyawar mu’amala tsakaninsa da jama’a.

Ya cigaba da cewar marigayi Malam Ladan Ayawa yana da kyakkyawan mu’amala da qabilu daban-daban, har mabiya addinai da dama, a duniya da ma qasar sa ta Najeriya, yace a qasar Amurka ma ya tava rayuwar jama’a da dama lokacin yana raye lokacin yana aiki da kuma bayan barinsa aiki.” A cewar sa.

Shugaban majalisar dattijai yace ko bayan mutuwar Malam Ladan Ayawa ayyukan sa na alheri zasu cigaba da wanzuwa tsawon lokaci ba a manta da shi ba ta vangaren aikin jarida.”

Shugaban majalisar dattijan, ya jajantawa gwamnatin Neja da masarautar Kontagora kan wannan babban rashin da aka yi.

Shugaban majalisar ya jajantawa gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello da abokansa na kusa da suka rasa wannan babban abokin na su.

Ahmed Lawan, ya roqi Allah da ya baiwa iyalan mamacin da ‘yan uwansa haqurin wannan babban rashin da su ka yi, ya kuma gafartawa mamacin yasa makomarsa ta zama Aljannar Firdausi.

Daga Muhammad Awwal Umar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *