Mayu Suka Kashe Jarumar Kannywood Asma’u Adam – Inji Wata Mijiya

Wata mijiya ta bayyana cewa akwai yiwuwar mayu ne sanadin mutuwar wata jarumar Kannywood mai suna Asma’u Adamu Abdullahi a watan jiya. Ita dai Asma’u, wadda a industiri aka fi sani da sunan Asma’u Adam, Allah ya ɗauki ran ta ne a ranar Asabar, 12 ga Yuli, 2020 a Asibitin Nassarawa da ke birnin Kano bayan ta yi fama da rashin lafiya.  Wata majiya ta kusa da jarumar ta shaida wa mujallar Fim cewa marigayiyar ta taɓa shaida mata cewa wannan rashin lafiyar da ta ke yi, mayu ne su ka kama ta. Majiyar ta ce kuma wannan ne sanadiyyar rasuwar tata. Asma’u ta rasu ta bar ‘ya’ya huɗu da kuma iyayen ta.  Marigayiyar ‘yar asalin Ƙaramar Hukumar Ɗambatta ce a Jihar Kano. Hasali ma dai mahaifin ta, Alhaji Adamu Abdullahi, shi ne Sarkin Fulanin Ɗambatta. 

Asma’u Adam (a tsaye) tare da ƙawar ta, jaruma Shalele Umar

 Mujallar Fim ta gano cewa fitaccen jarumi Shu’aibu Idris Lilisco shi ne ya kawo Asma’u cikin harkar fim tare da yardar iyayen ta, kuma ta cika dukkan ƙa’idojin shiga harkar kafin ta fara.  Da wakilin mu ya tuntuɓe shi kan lamarin, Lilisco ya bayyana Asma’u da cewa mace ce wadda ba ta da hayaniya, kuma ba ta da shige-shige, “ita sai dai kawai idan ka ga aikin ta ka kira ta, ta yi maka aiki ta tafi.” Marigayiyar ta fito a cikin shirin ‘Kwana Casa’in’ na gidan talabijin na Arewa24, kuma ta fito a fim ɗin ‘Kaico’ da fim ɗin ‘Umar’ da ma wasu.  Allah ya jiƙan ta da rahama, amin. 

Madogara: Fimmagazine

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *