Jigawa: An Umurci Kotuna Da Su Gaggauta Komawa Aiki


Babban mai shari’a na jihar Jigawa, mai shari’a Aminu Sabo Ringim ya umarci kotuna a fadin jihar nan da su gaggauta komawa bakin aiki don cigaba da sauraron shari’u.


A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mukaddashin Daraktan mulki da yada labarai na sashin shari’a na jihar Jigawa, Barista Auwalu Sani Balago, ta ce babban jojin ya bada umarnin ne biyo bayan bin ka’idoji da dokokin samun kariya daga cutar covid-19 wadda majalisar kula da al’amuran shari’a ta amince da su.


Ka’idojin sun hadar da yin feshin kashe kwayoyin cuta a kotuna da kuma horas da ma’aikatan shari’a matakan kariya daga cutar korona.
Mai shari’a Aminu Sabo Ringim ya kuma bukaci alkalai da wadanda suke zuwa kotu da sauran al’umma su rika amincewa da gwajin zafin jiki da amfani da takunkumin rufe fuska da wanke hannu akai-akai da bada tazara a lokacin shiga kotuna.


A halin da ake ciki kuma, mai shari’a Aminu Sabo Ringim ya bayyana cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin bangaren shari’a da hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomi ta jiha.


Babban jojin ya bayyana hakan ne lokacin da shugaban hukumar da ‘yan rakiyar sa suka kai masa ziyarar ban girma a Ofishinsa, inda yayi fatan dangantakar zata cigaba da wanzuwa.
Tun farko a nasa jawabin shugaban hukumar kula da ma’aikatan kananan hukumomin, Alhaji Uba Bala Ringim ya ce sun kai ziyarar ne a cigaba da ziyarar da yake kaiwa ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jiha dana tarayya domin kulla kyakkyawar dangantaka a tsakanin su da hukumar.


Alhaji Uba Bala ya bayyana bangaren shari’a amatsayin mataki na karshe na sharewa talaka hawaye, inda ya yabawa babban jojin bisa kokarin sa wajen daga martabar bangaren shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *