Mijina Ya Barmu Nida Ya’yana Saboda Idanun Mu Yana Kama Da Na Kyanwa (Mage).

Wata Mata a jihar Kwara mai suna Risikat ta koka akan cin mutunci da Mai gidan ta yakeyi musu ita da ya’yanta.

Matar ta ce Allah ya bashi haihuwa amma yace bayaso saboda wai sunada idan nun Mage.

Daga cikin ya’yansa yakori wata Yar sa Mai shekaru 8 Daga gidansa, kawai saboda halittar idanuwa yariyar suna kama da idanun Mage.

A lokacin da ya ke zantawa da manema labarai mutumin ya ce yakan kasa Bacci da nutsuwa a duk lokacin da yahada idanu da yarinyar domin idanun ta na haske kamar Mage.

Wanda hakan ke hanashi Barci duk da Nina haife ta bazan iya rayuwa nida ita a waje guda ba. Domin takan tsoratani a kullum in kasa samun nutsuwa injishi.

Daga Jaridar Wucin Gadi Media News

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *