An Bukaci Hukumar Shirya Jarabawa Ta WAEC Ta Sake Bitar Lokacin Jarabawa A Ranakun Juma’a (hotuna)

Hukumar shirya jarabawar kammala babbar sakandire ta WAEC ta sake sanya jarabawa a daidai lokacin da Musulmai daga cikin dalibai za su gabatar da sallar Jumma’a a cikin sabon jadawalinta na jarabawar da ta fitar ranar Litinin da ta gabata, kuma wacce za a fara sati mai zuwa, wato Talata 11 ga Agusta, 2020.

Sabon jadawalin da hukumar ta fitar ya ci karo da lokacin da Musulmai suke gabatar da ibadarsu ta sallar Jumma’a wanda kuma hakan za mu iya cewa da gangan aka yi, domin ba wannan ne karo na farko ba da suke saka lokacin jarabawar ta WAEC a ranakun Jumma’a a kuma daidai lokacin gudanar da ibadar.

Kungiyar Arewa Media Writers ta samu korafe korafe daga musulmai musamman ‘yan yankin na Arewa cewa hukumar ta WAEC ta tsaida lokacin da ake ibada, don haka muke ankarar da hukumar WAEC ta sani cewa sabon jadawalin da ta fitar kamar nuna wariya ne da nuna bangaranci ga musulmai.

Daga cikin jarabawar da aka sanya lokacinsu daidai da lokacin gudanar da sallar Jumma’a, suma dalibai wadanda suke Musulmai suna rubuta su. Saboda haka, a gaskiya akwai kalubale mai tarin yawa a cikin haka.

Yin hakan da hukumar ta yi har ya sa jama’a tunanin cewa WAEC tana yi ne da niyya kawai don son nisanta matasan Musulmai daga guraren ibadunsu. Tana sanya musu tsanani wajen su gabatar da ibadunsu yadda ya kamata.

Kuma hakan ya sa jama’a na ganin cewa Hukumar na yi ne kawai don ragewa matasan Musulmai kwarin gwuiwar gudanar da ibadunsu a lokutansu.

Lokacin da muka samu sanarwar cewa Hukumar ta fitar da sabon jadawalin jarabawar wannan shekara ta 2020, sai muka samu akwai cin karo tsakanin jarabawa guda uku da kuma lokacin sallar Jumma’a:

  1. Jarabawar Management–in–Living wacce dalibai za su zana a ranar Jumma’a 14 ga Agusta, 2020 da misalin ƙarfe biyu daidai (2:00pm)

2.. Jarabawar Literature–in–English wacce za su zana ranar Jumma’a ita ma 21 ga Agusta, 2020 da misalin ƙarfe biyu daidai (2:00pm); l

3.. Jarabawar Health Science wacce za su zana ta ita ma ranar Jumma’a 4 ga Satumba, 2020 da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana (1:30pm).

An yi haka duk kuwa da irin kiraye-kirayen da Hukumar Kare ‘Yancin Musulmi wato (Muslim Rights Concern, MURIC) take yi a kan kula da kiyaye irin wadannan cin karo da juna tsakanin jarabawar da kuma sallar ta Jumma’a, to, ya kamata a duba.

Wannan ba shi ne karo na farko da Hukumar ta sanya jarabawa ba a daidai lokacin gudanar da sallar Jumma’a, don haka cigaba da yin haka ba zai yi ma’ana ba, ya kamata hukumar ta tabbatar da yi wa kowanne sashi adalci.

Irin gwagwarmayar da MURIC ke yi wajen magana akan jarabawar da ake sakawa ranar Jumma’a ga Hukumar WAEC ba yanzu ne farau ba. Amma abin takaici Hukumar taki amsar abin da ya kamata na kiraye-kirayen da aka yi mata a baya.

A duk inda Musulmai suke a fadin duniya ba sa wasa da sallar Jumma’a. Ita wannan ibada ta sati-sati, wato sallar Juma’a tana da girma ne ga Allah (SWT) kuma wajiba ce kamar yadda ya zo a cikin Al-Ƙur’ani mai girma (Surãh ta 62, Ãya ta 9 zuwa ta 11). Kuma kin kiyaye ta ta kowace hanya na iya haifar da rauni ga bawa a wajen Allah (SWT).

Kuma a dokance idan WAEC za ta yi adalci ya kamata ta girmama lokutan salloli na Musulmai ba ma iya sallar Jumma’a ba, domin ranar Lahadi wacce take ranar ibadar ‘Kiristoci tana nan yadda take ba tare da wani ya isa ya canza ta ba.

Sannan duk da cewa MURIC ta yi kira ga fadar Tarayya da Hukumar bai daya ta ilimi akan wannan halin ko-in kula da WAEC ke yi ga dalibai Musulmai. To, ya kamata mu sani nan gaba babu wanda zai zargi dalibai Musulmai idan har basu rubuta jarabawar da aka saka musu ita a lokacin da yakamata a ce suna masallatansu na Jumma’a ba.

Duk jarabawar da za ta na tauye hakkin wani addini to, ta sabawa zamantakewa kuma babu girmama doka a ciki babu tsari kuma babu duba yanayi.

Sakon mu Arewa Media Writers ga Hukumar WAEC shine a gyara jaddawalin jarabawar WAEC kuma ta kiyaye irin haka a nan gaba domin baiwa kowane sashi hakkinsu.

Ya kamata WAEC ta rika la’akari da tsarin lokacin ibada, bama sai iya musulmai kadai ba, wanda a yanzu sune ake yi a lokutan su. Muna ganin idan aka gyara to, an yi adalci, kuma kowanne bangare zai sa a rana cewa ba a ware shi ba.

Da fatan za a gyara.

Daga Kungiyar Arewa Media Writers

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *