Ambaliyar Ruwa Ya Cinye Gidaje Sama Da 200 A Jihar Jigawa

Al’ummar kauyen Mai Rkumi dake karamar hukumar Malammadori a jihar Jigawa suna bukatar agajin gaggawa.

Kamar yanda za ku gani a cikin hotuna, Allah ya jarabce su da ibtila’in ambaliyar ruwa wanda ya yi sanadiyyar asarar gidade sama da dari biyu (200) a safiyar yau Alhamis bayan da aka kusan kwana ana ruwan sama kamar da bakin kwarya.

Wannan ne ya sa al’ummar wannna yanki suke neman agaji daga gwamnatin jihar Jigawa da kuma ta karamar hukumar Malammadori domin wadanda abubuwan ya shafa su samu matsugunin da za su rayu kafin Allah ya sa mu ga karshen wannna damina.

Daga Umar H. Maidoki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *