‘Yan Sanda Sun Kama Sojoji Masu Fashi Da Makami (hotuna)

Jarumin ‘dan sanda mai fasa taron dangin ‘yan ta’adda wato DCP Abba Kyari kwamandan rundinar FIB-Intelligence Response Team (IRT), ya samu nasarar farautar wasu gungun barayi ‘yan fashi da makami wadanda suka tare motar banki da ta yi dakon kudi na milyoyin naira suka kashe ‘yan sanda hudu dake rakiyar motar a jihar Ebonyi satin da ya gabata.

Cikin wadannan gawurtattun barayi ‘yan fashi wanda DCP Abba Kyari ya kama, akwai korarren soja da kuma sojan da yake aiki:
(1) Soja na farko ‘dan fashi, sunansa
Sajen (Sgt) Ayeni Samuel ‘dan shekara 43, yana da nambar aiki da rundinar sojin Nijeriya 03NA/53/088, yana aiki a Command Day Secondary School Nigerian Army Cantonment Ikeja Lagos, asalinsa mutumin Illesha, karamar hukumar Illesha South jihar Osun.

(2) Kofur (Cpl) Emeka Harrison, yana da lambar aiki da rundinar sojin Nigeria 03NA / 53 ‘dan shekara 33, rundinar sojin Nigeria ta koreshi daga aiki, kafin a koreshi daga aiki yana aiki a 8 Division Garrison, Maiduguri jihar Borno, asalinsa mutumin garin Nsukka ne, a karamar hukumar Nsukka East jihar Enugu, an koreshi daga aiki a shekarar 2015.

(3) Sai sauran abokan aikinsu ‘yan fashi mutum 5, bayan Abba Kyari ya kamasu sun amince da laifin da suka aikata na tare motar banki mai dakon kudi suka kashe ‘yan sanda 4, tare da sauran fashi da makami da garkuwa da mutane da suka aikata

Sannan Abba Kyari ya kwato makamai a hannun ‘yan ‘yan fashin, wadanda suka hada da, kayan fashewa wanda ake zargin bomb ne har guda 12 da suke fasa banki da su, bindiga kirar GPMG guda 1, bindiga kirar AK47 guda 6, magazine din bindigar AK47 guda 57, harsashin bindiga guda 1,620 motocin da suka kwace a hannun mutane guda 2, kayan balle kofa, da kuma kayan sihiri ko tsafi

Sannu da kokari Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari, ana nuna maka bakar hassada da kyashi kana kara karfi da kokari kare rayukan ‘yan Nigeria, jinjina gareka jan gwarzo jarumi💪 Allah Ya kareka daga dukkan sharri, Ya kai mana kai matsayin babban sufeta janar. Amin.

Daga Datti Assalafiy

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *