‘Yan Sanda Sun Kama Ma’aikatan Lafiya Da Masu Sayar Da Jarirai A Katsina (hotuna)

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinan ‘yan sanda Sanusi Buba, sun yi nasarar cafke wasu mata biyu, ma’aikatan jinya dake aiki a wani asibiti mai zaman kansa, da ake kira Okmos, da ke kan titin Yahaya Madawaki, cikin garin Katsina, inda wata ‘yar shekara ashirin da biyar, Shamsiyya Sani da ke garin Dandagoro, ta haifa ba tare da yin aure ba, kuma ta bar jaririn a asibitin ta gudu. Kuma ta rubuta takarda da hannunta cewa ta haife shine ba tare da aure ba.

Kakakin rundunar’yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isa ya yi baje kolin su ga manema labarai, a helkwatar rundunar da ke Katsina.

SP Gambo Isah ya ce rundunar’yan sanda ta yi nasarar cafke malaman jinya guda biyu akwai Misira S. Tijjani da ke zaune a Unguwar Canada Mai shekaru talatin da biyar da kuma Grace Ejigu, yar shekara arba’in da ukku, da ke zaune a Shagari Low-cost cikin garin Katsina, inda suka hada baki, suka saidawa wata Eucharia Onyema, da ke zaune a Sabuwar Kasuwa yar shekara arba’in da biyar. Allah ya toni asirin su akan hanyar zuwa gidajen su daga asibitin, tare da taimakon wani mai haya da Keke Napep. An cafke su a ranar 25/7/2020.

Rundunar yansanda ta jihar Katsina na cigaba da bincike, cewar Kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Katsina SP Gambo Isa.

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *