Matar Gwamna Masari Ta Dauki Nauyin Kula Da Lafiyar Mahaukaciyar Da Ta Haifi ‘Yan Biyu A Malumfashi

Matar Gwamna Masari Ta Dauki Nauyin Kula Da Lafiyar Mahaukaciyar Da Ta Haifi ‘Yan Biyu A Malumfashi

…ta kuma gina mata gida da masallaci a garinsu bayan ta warke

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Asiya Mohammad, wadda ke da lalurar tabin hankali da ta haifi ‘yan biyu a garin ‘Yanbita da ke karamar hukumar Malumfashi a jihar Katsina. Yanzu haka ta warke garas, har matar Gwamna Aminu Bello Masari, Hajia Hadiza Masari ta gina mata gida mai daki biyu da Masallaci a mahaifarta ta garin Unguwar Kuka da ke cikin karamar hukumar Kankara.

Mohammad Garba, Mataimakin na musamman kan kafafen sadarwa na zamani, mai kula da yankin Funtua, wanda kuma shi ne kan gaba wajen samun nasarar warkewarta da kuma abun alherin da aka yi mata ya shaidawa RARIYA ta waya.

Mohammad Garba ya kara da cewa a shekarar da ta gabata ne, Asiya Mohammad ta haifi yan biyu, wanda hotunan sukai ta yawo a kafafen sadarwa na zamani, har Allah ya sa abun ya kai ga uwar gidan Gwamna, Hajia Hadiza Masari, inda ta bada umurnin a kai ta asibitin masu lalurar tabin hankali, bayan kwashe watanni ana kula da ita, har Allah ya bata lafiya ta warke garas, kuma yanzu haka an gina Mata gida a garin Unguwar Kuka, har da masallaci. An kuma bata jari, wanda za ta iya dogaro da kanta. Kuma yan biyu da ta haifa suna nan cikin koshin lafiya.

Idan dai za’a iya tunawa RARIYA ta ba da rohotan haihuwa da Asiya Mohammad ta yi a ranar sha biyar ga watan Yuli na shekarar da ta gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *