Matasan Arewa Sun Goyi Bayan Mulki Ya Koma Kudu

Rahotanni sun bayyana cewa matasan Arewacin Nijeriya sun shawarci jam’iyyun siyasa a kasar dasu yi watsi da kiran jingine karba-karba wurin fitar da ‘yan takarar shugaban kasar a zaben 2023.

Matasan karkashin inuwar AYPS sun yi kiran ne bayan dan wan Shugaba Buhari, Mamman Daura ya bayyana ra’ayinsa cewa a jingine tsarin a koma bin cancanta a zaben shugaban kasa na 2023.

Shugaban kungiyar matasan mai rajin wanzar da tsaro da zaman lafiya, Salisu Magaji, ya ce a bari mulki ya koma yankin Kudu a zaben mai zuwa domin tabbatar da dunkulewar kasar a mulkin demokradiyya.

Kungiyar ta ce babu adalci ada da tsarin na karba-karba ba tare da yankin Kudu ya amfana da shi ba a shugabancin kasar.

“Muna goyon bayan a mayar da shugabancin kasa zuwa Kudu a 2023 saboda yankin na da dama da kuma ‘yan takarar da suka dace.

“Matsayarmu ita ce yankin Arewa ya mara musu baya domin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar.

“Muna ganin idan Arewa ta ci gaba da mulki bayan gwamnatin Buhari na biyu, to hakan zai yi illa ga zaman lafiyar kasar.

“Muna bayar da shawara ga yankin Arewa ya koma gefe ya mara wa Kudu baya ya gaji Buhari. Sadaukar da kai ne da ya kamata mu yi”, inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *