‘Yan Bindiga Sun Kwace Fursinoni A Hannun Jami’an Gidan Yari A Filato

Wasu ‘yan bindigasun yi wa jami’an lura da gidan yari kwanton bauna inda suka kwace wadansu fursunoni a hannunsu.

‘Yan bindigar sun kari harin ba zata ne a wata kotu a karamar hukumar Barikin-Ladi a jihar Filato a ranar Alhamis, inda suka farmaki tawagar motoci dauke da wadanda ake tuhuma da fashi, fyade ko kuma satar mutane har mutum 14.

Shafin yanar gizo na Sahara Reporters ya bayyana cewa hakan ya auku ne a jiya Alhamis da rana a lokacin da ‘yan bindigar suka zo tare motocinsu da kuma bindigogi kirar AK 47 da wasu makamai na zamani da na gargajiya. Inda Suka kwace akalla mutum 6 daga cikin wadanda ake tuhuman 14 da suke hannun gandrobobin, suka tafi da su a cikin motocin da suka zo da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *