Wata Matashiya Ta Yi Ikirarin Samun Ciki Ba Tare Da Saduwa Da Da Namiji Ba

Wata matashiya ta yi ikirarin samun ciki ba tare da saduwa da Namiji ba

Wata mata ta yi ikirarin samun ciki ba tare da Namiji ya sadu da ita ba.

Samantha Lynn Isabel wadda a yanzu ke da shekaru 26 tace lokacin tana da shekaru 19 ne lamarin ya faru.

Ta bayyana hakane a kafar Tiktok wanda ya dauki hankula sosai. Tana da yaro dan shekaru 5 wanda tace ba zata iya yin bayanin yanda ta samu cikinsa ba.

Tace a wancan lokacin tana da Saurayi amma kuma basu taba saduwa ba, saidai shafe-shafe. Tace kwatsam sai ta ganta da ciki.

Tace abin ya bata mamaki ta je ta gaya masa shima yayi ta mamaki amma duk da haka yayi farin ciki inda yace zai zama uba.

Dan nata sunansa Bentley inda kuma sun samu wani yaron me suna Theo. Tace a wancan lokacin ta rika tunanin ta yaya zata haihu tunda gata sabuwar budurwa fil.

Tace abokanta sun rika tsokanarta da ce mata Maryam.

Wata Likita, Dr. Jennifer Lincoln ta bayyanawa Buzzfeed cewa hakan zai iya faruwa saboda ba lallai sai an yi Jima’I za’a iya daukar ciki ba, tace idan akwai maniyyi a hannun saurayin kuma ya saka yatsarsa cikin al’aurar macen to zata iya yiyuwa a samu ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *