Wasu Matasa 2 ‘Yan Shekaru 20 Wadanda Suka Yiwa Matar Makwabcinsu Fyade Kafin Suka Kashe Ta Sun Shiga Hannu

‘Yan Sanda a jahar Katsina sun cafke wasu Matasa 2, Faisala Lawal Da abokinsa Abba Nasiru a kan zargin yiwa matar makwabcinsu fyade Tare Da kashe ta bayan sun aikata fyaden.

A wani sanarwa da kakakin ‘yan sanda na jahar ya fitar, SP Gambo Isah, ya ce wadanda ake zargi sun kasance Yan Shekaru 20, a 11 ga watan Mayu 2020 wadanda ake zargi suka aikata laifin a yayin da suka tsallake katangar makwabcinsu suka kama matarsa suka yi ma ta fyaden gayya bayan sun gama sai suka Gano ta gano daya daga cikin su a nan ne suka yanke hukuncin kashe ta a nan take ta hanyar yi ma ta yankar rago


“A ranar 11 ga watan Mayu a lokacin Watan Ramadan da misalin karfe 1:00 na dare wadanda ake zargi Faisal (dan Shekaru 20) tare da Abba Nasiru (Dan Shekaru 20) suka tsallaka ta katangar makwabcinsu Lawal Adamu Suka Yiwa matarsa, Hajiya Adam, fyade. Da suka gane matar ta gano fuskar daya daga cikinsu sai suka yanke hukuncin yi kashe ta ta hanyar Yi ma ta yankar rago.” Kamar yadda aka ruwaito a sanarwaR

Gambo ya ce an Gano wayar hannun Matar da aka kashe a hannun daya daga cikin wadanda Ake zargi, Nasiru. Inda ya ce yan sanda sun gano rigar daya daga cikin wadandA ake zargi, Lawal Da jini

Kakakin ya ce za a caje wadanda ake zargi zuwa kotu a kan zargin aikata kisa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *