Obasanjo Ya Lakaɗa Wa Matar Ɗan Uwansa Dukan Tsiya Saboda Zargin Ta Sace Masa Kuɗi

Tsohon Shugaban Ƙasar Najeriya, Olesegun Obasanjo, ya lakaɗa wa matar ɗan uwansa duka saboda zargin ta sace masa wasu kuɗaɗe.

A cewar wani rahoton shirin In Da Ranka na Freedom Radio, Kano da Labarai24 ta bibiyi maimaicinsa ranar Alhamis, wannan al’amari ya faru ne a yankin Iffo Ibogun.

Rahoton ya ce Mista Obasanjo ya shiga yankin da mota cike da jami’an tsaro, bayan da ya zargi matar ɗan uwansa, Adebayo Molaje da sace masa zunzurutun kuɗi har naira miliyan N160.

Rahoton ya ƙara da cewa Mista Obasanjo ya fita ne daga gonarsa dake Otta da misalin ƙarfe 5:00 na Asuba, lokacin da mafi yawan mutanen yankin ba su tashi daga bacci ba.

Yana shiga sai aka ji yana Omolaja ole, Abiodun ole, hakan ne yasa matar ta fito don ta ga wane ne yake kira.

Tana fitowa sai suka yi ido huɗu da tsohon Shugaban Ƙasar, nan take yasa jami’an tsaronsa suka zagaye ta, inda ya zaro wata zabgegiyar bulala ya fara zabga mata, ya zane ta tas ba tare da ta iya guduwa ba.

Bayan ta sha bulalar ne sai aka tambaye ta ko ita ta ɗauki waɗannan kuɗaɗe, sai ta ce ita sam ba ita ta ɗauke su ba, ta ce tsohon Shugaban Ƙasar sharri kawai ya yi mata.

Wani da abin ya faru a gaban idonsa, wanda kuma ya buƙaci a sakaye sunansa, ya ce: “Ba mu taɓa ganin irin wannan hukunci a yankinmu ba, inda babban mutum kamar Obasanjo ya jagoranci yanke hukunci da kansa duk da cewa zai iya sa wani ko kuma mijin nata, wanda yake ɗan uwansa ne na jini, ya yi masa bincike a kan laifin da ta aikata masa”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *