Maigadi Dan Shekaru 23 Ya Yiwa ‘Yar Shekara 7 Fyade A Kontagora

‘Yan Sanda a karamar hukumar Kontagora, jahar Neja sun kama wani matashi Dan Shekaru 23, Johan Adamu, Mai zama a unguwan Nasarawa dake garin Kontagora a kan zargin yiwa yarinya Mai zama a wani unguwar yar Shekaru 7 Fyade

‘Yan Sanda sun cafke wanda ake zargi a ranar 16 fa watan Yuli, 2020.

Shi wanda ake zargi ya furta shigan yarinyar ta baya a inda yake aikin gadi. Kakakin rundunar yan sanda na jahar Wasiu. Ya ce za a caje wanda ake zargi zuwa kotu ba tare da bata lokaci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *