Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Ma’aikatanta Da Su Yi Gwajin Korona

Jaridar Punch ta labarto cewa; gwamnatin tarayya ta buƙaci ma’aikatan gwamnati da ke zaune a Abuja da su je a yi musu gwajin cutar korona.

Hakan ya fito ne a wata sanarwa daga ofishin Babbar Sakatariya kan jin daɗin ma’aikata ta gwamnatin tarayya, Dakta Evelyn Ngige inda ta buƙaci ma’aikatan da su je a yi musu gwajin

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samar da kayayyakin gwajin cutar ta korona a wani wuri da ake kira ThisDay Dome dake Mohammed Kur Avenue a birnin tarayya Abuja.

Sannan za a rinƙa gudanar da gwajin ne da misalign karfe 10:00 na safe zuwa 4:00 na yamma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *