Dan Shekaru 44 Ya Yiwa Wata Karamar Yarinya Nakasassa Fyade A Yola

Rundunar ‘yan sanda reshen jahar Adamawa sun cafke wani Dan Shekaru 44, Ezekiel Mahai, a kan zargin yiwa wat karamar yarinya nakasassa fyade

A cewar Kakakin rundunar ‘yan sandar jahar, DSP Suleiman Nguroje, Mahai ya yiwa yarinyar fyade ne a kauyen Prakwanta dake karkashin karamar hukumar Gimbiya. An samu labarin cewa Mahai sai da ya bari mahaifiyar yarinyar ba ta gida kafin ya Je ya yi ma ta fyade.

”A halin yanzu ita Yarinyar Da Aka yiwa fyade tana asibiti ana mata magani a yayin da yan sanda suka cafke wanda ake zargi kafin a gurfanar Da shi a gaban kotu.” Nguroje ya fadawa manema labarai

Hakan ya faru ne kwana biyu bayan wani magidanci ya furta yiwa yarsa Yar Shekaru 9 Fyade a birnin Yola

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *