An Yi Kira Ga ‘Yar Abacha Haj. Fatima (Gumsu) Da Ta Fito Takarar Kujerar Sanatan Kano

Wata kungiyar matasan jihar kano da sukayi taro a sakatariyar Audu bako dake nan kano sunce Hajiya Fatima abacha CE ta cancanci wakiltar kano ta tsakiya a zaben 2023 me zuwa duba da yadda mata suke da tausayi.

Shugaban matasan comarede zubairi yace yanzu lokaci yayi dazasu farka daga bacci Susan inda suka dosa a siyasance don haka wannan karan kuma mace zasu gwada a kano ta tsakiya.

Yakara da cewa Fatima abacha tanada kwarewa suna Sa ran zatayi abinda yawancin mazan dasuka wakilci kano ta tsakiya basuyi ba domin Fatima abacha tanada tausayi gata da son ganin rayuwar talaka ta inganta.

Shugaban kungiyar yace kira sukeyi GA Hajiya Fatima abacha data amsa wannan kira nasu kuma suna fatan zataji wannan kira nasu a matsayinsu Na matasa.

Taron dai yasamu halartar shugabannin kana nan hukumomi 15 ns kano ta tsakiya Wanda ya gudana a sakatariyar Audu bako dake nan kano.

Daga Kabiru Ado Muhd.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *