An Gudanar Da Taron Samar Da Hanyar Dakile Matsalolin Fyade Da Cin Zarafin Yara

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa a jihar Jigawa ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki domin dakile matsalalolin fyade da cin zarafin kananan yara a jihar Jigawa.
A jawabin da ya gabatar Daraktan hukumar, Malam Shu’aibu Haruna Karamba ya ce an shirya taron ne domin neman shawarwari yadda za`a fadakar da al’umma illolin fyade a cikin al’umma.
Malam Shu’aibu Haruna Karamba ya kara da cewa ana hasashen samun nasara bisa la`akkari da yadda mahalarta taron suka bada hadin kai da goyon baya.
Shima a jawabinsa kwamishinan shari’ah na jihar Jigawa, Dakta Musa Adamu Aliyu ya ce gwamnatin jiha ta maida hankali wajen dakile matsalar fyade a wannan jiha.
Dakta Musa Adamu Aliyu yace kofarsu a bude take domin karbar shawarwari da zasu taimakawa gwamnati wajen samun nasarar yaki da wannan mummunar dabi’a.