Ina Da Baiwar Waka Sai Dai Na Boye – Ali Nuhu

Daya daga cikin manyan Jaruma masaantar shiry Fina-finan Hausa na Kannywood, Jarumi Ali Nuhu, ya bayyana cewar yana da wata boyayyar baiwa kuma wannan baiwar ita ce waka.

Babban Jarumin kuma wanda ake yima lakabi da sarki Ali Nuhu, ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da manema Labaru a cikin shirin daga bakin mai ita.

A lokacin da yake amsa tambayar cewar baya ga shirin Fina-Finai shin yana da wata boyayyar baiwa, a take ya bayyana cewar yana da boyayyar baiwar Waka.

Zuwa yanzu dai Jarumi Ali Nuhu, baa taba gani ko kuma sauraren wata wakar daya rera da kan sa ba, sai dai an taba hangen sa a wata waka da Jarumi Adam A Zango, ya rera kuma suka fito a bidiyon wakar a tare a Jihar Kaduna.

Mai zaku ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *