COVID-19: Gwamnatin Jihar Kano Ta Hana Hawan Sallah

Majalisar Zartarwa ta Jihar Kano ta hana Hawan Salla a dukkan masarautu biyar na jihar saboda cutar COVID-19.
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Muhammad Garba ya sanar da haka ranar Laraba da safe a yayin taron manema labarai a ofishinsa, kamar yadda Kano Focus ta rawaito.
Mista Garba ya ce dukkan sarakuna biyar na jihar Kano za su yi Sallar Idi ne a masarautunsu, bisa bin matakin kariya daga COVID-19 sau da ƙafa.
Har yanzu Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero bai yi Hawan Salla na farko ba saboda COVID-19.