Buhari Ya Fi Kowane Shugaban Afirka Yawan Mabiya A Shafin Tiwita; Trump Ya Fi Saura A Duniya – BCW

Wata cibiyar harkokin sadarwa ta duniya, Burson Cohn and Wolfe (BCW), a wani bincike da ta yi ta gano cewa Shugaba Muhammadu Buhari ne shugaban da ya fi sauran takwarorinsa na Africa yawan mabiya a shafin sada zumunta na Tiwita da adadin mabiya miliyan uku da dubu dari da ashirin da daya da dari da sittin da tara (3,121,169).

Cibiyar ta fitar da wannan bincike nata a cikin kundinta na nazari na shekarar 2020.

Mai bi wa Shugaba Buhari shi ne shugaba Paul Kagame na Rwanda, wanda ke da adadin mabiya miliyan daya da dubu dari tara da goma da dari da hamsin da tara (1,910,159)

Na ukunsu kuma shi ne Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu, wanda mabiyansa ke ci gaba da karuwa cikin shekara guda da ta gabata, inda ya yanzu adadin mabiyansa na tiwita ya kai miliyan daya da dubu dari uku da tamanin da shida da dari takwas da arba’in da tara (1,386,849)

Binciken na BCW ya nuna cewa shekaru hudu a jere Shugaba Donald Trump ne ke kan gaba wajen yawan adadin mabiya a tiwita a duniya da adadin mabiya miliyan tamanin da daya da doriya.

Mai bi wa Donald Trump a duniya kuma shi ne Firayi Ministan Indiya, Narendra Modi, inda adadin mabiyansa na tiwita yanzu haka yaa kai miliyan hamsin da bakwai da digo tara.

Paparoma Francis ne ke bi wa Narendra Modi da adadin mabiya miliyan hamsin da daya a shafukansa daban-daban har guda 9 da ya ke da su a tiwita.

A nahiyar turai kuwa, Shugaba Emmanuel Macron ne aka gaba a yawan mabiya a tiwita da adadin mabiya miliyan biyar da dubu dari biyu da casa’in da uku da dari uku da arba’in da shida (5,293,346). Sai kuma shafin fadar gwamnatin Faransa ta Elysee Palace da ke da mabiya miliyan biyu da dubu dari hudu da casa’in da biyu da dari hudu da sittin da takwas.

Na uku a yankin turai shi ne Firayi Ministan Spaniya, Pedro Sanchez, mai adadi mabiya miliyan daya da dubu dari hudu da biyar da dari hudu da tamanin da daya.

Zuwa ranar i ga watan Yuni, 2020, adadin shafukan shugabannin duniya na kashin kansu da na fadojin gwamnati-gwamnati har guda dubu daya da tamanin da tara na da adadin mabiya miliyan dari shida da ashirin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *