Gwamnatin Zamfara ta musanta batun baiwa ƴan bindiga shanu bibbiyu don fansar AK47

Gwamnatin jihar Zamfara ta musanta Labaran da kafafen yada labarai suka bayar cewar gwamna Bello Matawalle ya sha alwashin bai wa ‘yan bindiga Shanu bibbiyu a matsayin fansar Bindiga AK47 ga yan ta’addan da ke addabar yankin.

To sai dai gwamnatin jihar ta ce za ta bada shanu 2 ga kowane dan bindiga daya aje makami domin ya cigaba da rayuwa.

Tuni dai batun ya janyo cece-kuce ganin yadda ko a baya makudan kudin da gwamnati ta baiwa ‘yan bindigar bai hanasu ci gaba da kai hare-hare ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *